Rivers: Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Gatan da Za Ta Yi Wa 'Shugaban Rikon Kwarya'

Rivers: Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Gatan da Za Ta Yi Wa 'Shugaban Rikon Kwarya'

  • Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa za ta ba sabon shugaban riƙon ƙwarya na jihar Rivers kuɗi daga asusun tarayya
  • Ministan shari'a, Lateef Fagbemi ya bayyana cewa za a sakarwa sabon shugaban na jihar Rivers kuɗin idan har ya buƙaci hakan
  • Lateef Fagbemi ya kuma kare matakin da shugaban ƙasan ya ɗauka na sanya dokar ta ɓaci a jihar mai arziƙin man fetur
  • Ministan ya nuna cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi ƙoƙarin shawo kan rikicin cikin maslaha amma ɓangarorin biyu su ka ƙi yarda

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi magana kan sakin kuɗaɗen jihar Rivers ga sabon 'gwamnan riƙon ƙwarya'.

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za a saki kason kuɗin jihar Rivers na wata ga Vice Admiral Ibok Ibas (mai ritaya).

Gwamnatin tarayya za ta saki kudin Rivers
Gwamnatin tarayya za ta ba gwamnan rikon kwarya na Rivers kudade Hoto: @ImranMuhdz
Asali: Twitter

Miinistan shari’a, Lateef Fagbemi, SAN, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a ranar Laraba, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Ba jira: Ministan Tsaro, Matawalle ya fadi shirin sojoji kan dokar ta baci a Rivers

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan ya kuma ce sanarwar sanya dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya yi a jihar Rivers ta zo a kan gaba, domin hana barkewar rikici a jihar, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

Gwamnatin tarayya za ta saki kuɗin Rivers

Yayin da yake amsa tambaya kan ko gwamnatin tarayya za ta saki kason kuɗin jihar daga asusun tarayya bayan sanya dokar, ministan ya ce idan gwamnan riƙon ƙwaryar ya nemi kuɗin, za a ba shi.

“A ganina, sakin kuɗaɗen yana da kyau, domin yanayin da ake ciki yanzu ya sa abubuwa sun sauya daga yadda al'amura suke gudana a baya."

- Lateef Fagbemi

Minista ya goyi bayan shugaba Bola Tinubu

Ministan ya kare matakin da Shugaban ƙasa ya ɗauka na ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers.

"Mun shafe kusan shekaru biyu da wannan gwamnati ke mulki a jihar Rivers."
“To yanzu, a wane lokaci kake ganin ya kamata shugaba Tinubu ya ɗauki mataki? Shin sai komai ya lalace? Ni ba haka na ke gani ba."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya sa labule da 'shugaban riko' na jihar Ribas, bayanai sun fito

“Ina ganin Shugaban ƙasa ya ɗauki mataki a kan kari. Ya bai wa dukkan bangarorin da abin ya shafa dama su gyara. Kafin hakan ma, ya kira su ya yi ƙoƙarin sasanta su."

- Lateef Fagbemi

Matawalle ya magantu kan dokar ta ɓaci a Rivers

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya goyi bayan dokar ta ɓaci da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya a jihar Rivers.

Ministan ya bayyana cewa matakin da shugaban ƙasan ya yi daidai domin dawo da doka da kwanciyar hankali a.jihar mai arziƙin man fetur.

Bello Matawalle ya bayyana cewa sojojin Najeriya na cikin shirin ko-ta-kwana domin kare muhimman kayayyakin gwamnati a jihar.

Ya yi gargaɗi ga masu shirin tayar da hargitsi da su shiga taitayinsu domin sojoji ba za su lamunci hakan ba ko kaɗan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng