Dangote Zai Bar Saida Fetur a Najeriya, NNPCL Ya Tsaida Yarjejeniyar Ciniki da Naira
- Matatar Dangote za ta dakatar da sayar da kayayyakin man fetur a cikin Najeriya saboda an daina sayar mata da danyen mai a Naira
- Wannan mataki ya biyo bayan yadda tattaunawar sabunta yarjejeniyar sayar da danyen man ya ci tura tsakanin NNPCL da Dangote
- Amma rahotanni sun ce matatar na ci gaba da safarar mai da ya ke sarrafa wa zuwa wasu kasashen waje, inda take samun daloli
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos - Matatar Dangote za ta dakatar da sayar da kayayyakin man fetur a kasuwar Najeriya, saboda tattaunawa kan sabon yarjejeniyar sayar mata da danyen mai a Naira ya ci tura.
Sai dai majiyoyi sun tabbatar da cewa matatar za ta ci gaba da sayar da kayayyakin man fetur ga kasashen waje, kasancewar ta na sayo danyen mai daga kasuwannin duniya da Dala.

Asali: Facebook
A labarin da ya kebanta ga The Cable ya nuna dama matatar Dangote na sayar da man fetur a kan Naira a Najeriya ne saboda ta na sayen danyen mai da kudin kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matatar ta dauki matakin bayan yarjejeniyarta da kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya zo karshe, kuma ba a kai ga sabunta ta ba.
NNPCL ya daina sayarwa Dangote danyen mai
A ranar 10 ga Maris, jaridu suka ruwaito cewa kamfanin NNPCL ta daina mutunta yarjejeniyar sayar da danyen mai ga matatar Dangote a kudin Naira.
Sai dai, 'yan sa’o’i bayan rahoton, Olufemi Soneye, babban jami’in hulɗa da jama’a na NNPCL, ya bayyana cewa yarjejeniyar da ta fara aiki tun Oktoba 2024 za ta ƙare ne a ƙarshen watan Maris.

Asali: Getty Images
Soneye ya ƙara da cewa ana ci gaba da tattaunawa domin sabunta yarjejeniyar da za ta bayar damar ci gaba da sayar wa Dangote danyen mai a Naira.

Kara karanta wannan
"Ba ka yi mana adalci ba," NLC ta yi raddi ga Obasanjo kan mafi karancin albashin N70,000
Yadda NNPCL ya sayarwa Dangote mai
Kakakin NNPCL ya bayyana cewa kamfanin ya sayar da ganga miliyan 48 na danyen mai ga matatar Dangote tun daga Oktoba 2024.
Ya ƙara da cewa, tun bayan fara aiki a 2023, gwamnati ta samar da ganga miliyan 84 na danyen mai ga matatar Dangote.
Gwamnatin tarayya dai ta rika sayar wa da matatun cikin gida danyen mai a Naira saboda tabbatar da wadatar man fetur a Najeriya.
Haka kuma matakin zai taimaka wajen samun damar adana Dalolin da ake kashe wa wajen shigo da danyen mai zuwa Najeriya.
Kotu ta shiga tsakanin NNPCL da Dangote
A wani labarin, kun ji cewa babbar kotun tarayya ta yi zama kan takaddamar da ake yi tsakanin kamfanin mai na NNPCL kan hana matatar Aliko Dangote shigo da danyen man fetur Najeriya.
Mai Shari’a Inyang Ekwo da ya yanke hukuncin, ya kori karar da NNPCL ya shigar, bisa dalilan da su ka hada da cewa babu gamsassun hujjojin da za a hana Dangote shigo da danyen mai.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng