"Za a Ƙaro Abu 1," Majalisa Za Ta Yi Gyara a Tsarin Auren Addinin Musulunci da Gargajiya

"Za a Ƙaro Abu 1," Majalisa Za Ta Yi Gyara a Tsarin Auren Addinin Musulunci da Gargajiya

  • Majalisar dokokin jihar Osun ta amince da kudirin doka na gyara tsarin auren Musulmi da na ƴan gargajiya, ya tsallaka zuwa karatu na biyu
  • Sabon kudirin dai zai kawo gyara a yanayin auren Musulmi ta yadda za a rika ba ma'aurata takardar shaidar aure a hukumance a jihar Osun
  • A zaman ƴan Majalisar na ranar Talata, 18 ga watan Maris, 2025, sun tafka mahawara kan kudirin kafin amincewa ya kai karatu na biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Osun - Majalisar Dokokin Jihar Osun ta fara yunkurin yin gyara a tsarin aure na addinin Musulunci da kuma na masu bin tsarin gargajiya.

Kudirin dokantar da tsarin auren da Musumai da yan addinin gargajiya ke yi ya tsallaka karatu na biyu a Majalisar dokokin jihar ta Osun.

Majalisar dokokin Osun.
Majalisar Dokokin Osun ta fara yunkurin gyara tsarin Auren musulmi da na ƴan gargajiya Hoto: Osun State House of Assembly
Asali: Twitter

Daily Trust ta tattaro cewa ƴan Majalisar sun amince da kudirin gyara tsarin auren ne a zamansu na ranar Talata, 18 ga watan Maris, 2025.

Kara karanta wannan

Majalisa ta hargitse ana shirin tattauna maganar dakatar da Gwamna Fubara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar dokokin Osun za ta gyara tsarin aure

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa dan majalisar da ke wakiltar mazabar Osogbo, Bamidele Lawal, ya bukaci majalisar da ta hanzarta amincewa da dokar.

Da yake gabatar da mahimman abubuwan da dokar ta ƙunsa, Lawal ya bayyana cewa dokar, idan an amince da ita, za ta bada damar ba da takardar shaida ga masu yin auren Musulunci da na gargajiya.

Wannan takardar za ta zama ingantacciyar hujja da za a iya amfani da ita wajen samun takardu na ƙasashen waje da sauran al'amura da ake buƙatar shaidar aure a dokance.

Za a naɗa magatakardar aure a kotun Osun

A cewarsa, dokar za ta tanadi naɗa rajistara na aure, wanda zai kasance ƙarƙashin ikon Shugaban kotun kwastamare ta jihar Osun.

Wannan rajistara ne zai riƙa bayar da lasisi da takardun shaidar aure ga ma’auratan da suka yi aure ta hanyar addinin Musulunci ko addinin gargajiya.

Kara karanta wannan

An gano inda Gwamna Fubara yake bayan sojoji sun mamaye fadar gwamnatin Ribas

Dan majalisar ya ƙara da cewa takardar da wannan rajistara zai bayar za ta kasance hujja da hukumomin Najeriya da na ƙasashen waje za su amince da ita.

Taswirar Osun.
Majalisar Dokokin Osun ta fara yunkurin gyara auren musulmi da ƴan gargajiya Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Kudirin dokar ya tsallaka karatu na 2

Bayan jin ra’ayoyin ‘yan majalisar, Kakakin majalisar dokokin Osun, Adewale Egbedun, ya goyi bayan kudurin dokar tare da sauran ‘yan majalisar.

Daga nan ne aka amince da dokar ta tsallaka zuwa karatu na biyu, sannan aka dage zaman majalisar zuwa ranar Laraba, 19 ga watan Maris, 2025.

Idan majalisar ta kammala karatu kan kudirin kuma ta amince da shi sannan gwamna ya rattaɓa masa hannu, daga nan ya zama doka a kan al'ummar jihar Osun.

Sultan na shirin musuluntar da Najeriya?

Kun ji cewa Majalisar Koli ta addinin Musulunci watau NSCIA ta karyata raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa Mai Alfarma Sarkin Musulmi , Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, na yunkurin musuluntar da Najeriya.

Kara karanta wannan

Majalisar Tarayya ta kare matakin sauke gwamnatin Ribas na watanni 6

A cikin wata sanarwar NSCIA ta fitar, ta bayyana cewa wannan zargi da ake jinginawa mai alfarma sarkin Musulmi ba shi da tushe balle makama.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng