Cikakkun Sunaye: Obi Da Sauran Masu Filaye 165 Da Wike Ya Kwace a Abuja

Cikakkun Sunaye: Obi Da Sauran Masu Filaye 165 Da Wike Ya Kwace a Abuja

Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ya soke takardun wasu filaye 165 a Abuja saboda rashin bunkasa su.

Sakataren dindin na birnin tarayya, Olusade Adesola, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Alhamis, 21 ga watan Satumba, jaridar Premium Times ta rahoto.

Wike ya kwace filayen wasu mutane a Abuja
Cikakkun Sunaye: Obi Da Sauran Masu Filaye 165 Da Wike Ya Kwace a Abuja Hoto: Nyesom Wike/Mr Peter Obi/Liyel Imoke
Asali: Facebook

Filayen da abun ya shafa suna a yankunan Maitama, Gudu, Wuye, Katampe Extension, Wuse 2, Jabi, Utako, Idu Industrial Zone, da Asokoro.

Ga jerin filayen guda 165 da masu shi.

  • Dan takarar shugaban kasa na Labour Party (LP), Peter Obi
  • Tsohon gwamnan jihar Cross River, Liyel Imoke
  • Tsohon ministan tsare-tsare na kasa, Udo Udoma
  • Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Ufot Ekaette
  • Tsohon sanatan Edo ta arewa, Victor Oyofo
  • Marigayi mawallafin jaridar Leadership, Sam Nda-Isaiah
  • Tsohon alkalin kotun koli, Niki Tobi
  • Tsohon Atoni Janar na tarayya, Kanu Agabi
  • Chidinma, Matar tsohon ministan sufurin jiragen sama, Osita Chidoka
  • Paul Nwabiukwu, hadimin darakta janar na WTO, Ngozi Okonjo-Iweala
  • Julius Berger Nigeria
  • Honeywell Construction Limited
  • BUA

Kara karanta wannan

Ainahin Dalilin Da Yasa Wike Ya Soke Filayen Peter Obi, BUA Da Sauransu a Abuja

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Duba cikakkun jerin sunayen a nan.

Wike ya kwace filayen tsoffin gwamnonin PDP uku

A gefe guda, mun ji a baya cewa akalla tsoffin gwamnonin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) uku ne suka rasa kadarorinsu, yayin da hukumar babban birnin tarayya (FCTA) a karkashin jagorancin Nyesom Wike ta kwace filayensu.

A ranar Alhamis, 21 ga watan Satumba ne hukumar FCTA ta bayar da umurnin kwace filayen a cikin wata sanarwa da aka buga a jaridu, tana mai bayyana cewar an soke su ne saboda sun ki bunkasa filayen ko kuma saba doka a babban birnin tarayya.

Ministoci: Watakila Wike ya karbe takardun filaye, ruguza gine-gine 6,000 a Abuja

A wani labarin, Legit Hausa ta kawo cewa akwai yiwuwar gwamnatin tarayya ta shiga unguwanni akalla 30 kuma ta sauke gine-ginen da sun fi 6, 000 idan ana so a gyara Abuja.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Sabon Gwamnan CBN Ya Kama Aiki Gadan-Gadan Tare da Mataimaka 4, Bayanai Sun Fito

Wani rahoton da Punch ta fitar ya bayyana cewa muddin ana sha’awar dawo da tsarin birnin tarayya, za a rugurguza gine-gine masu dinbin yawa.

Jim kadan bayan rantsar da Nyesom Wike a matsayin ministan babban birnin, ya tabbatar da cewa zai yi rugu-rugu da duk ginin da ya sabawa tsari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel