Aiki ga Mai Yin Ka: Yadda Hukumar EFCC Ta Kwato N365.4bn
- Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta bayyana nasarorin da ta samu a cikin shekarar 2024 da ta gabata
- Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa sun samu nasarar ƙwato N365.4bn a 2024
- Olukoyede ya bayyana cewa sun samu wannan nasarar ne sakamakon jajircewa da sadaukarwar ma'aikatan hukumar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Akwa Ibom - Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da ta'annati da dukiyar ƙasa (EFCC) ta bayyana kuɗaɗen da ta ƙwato a shekarar 2024.
Hukumar EFCC ta ce ta ƙwato sama da Naira biliyan 365.4 tare da samun nasarori 4,111 a kotu a shekarar 2024 da ta gabata.

Asali: Facebook
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar EFCC, Dele Oyewale, ya fitar a ranar Lahadi a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
EFCC ta samu nasarori a shekarar 2024
Oyewale ya ce shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ne ya bayyana hakan a Uyo, jihar Akwa Ibom, a ƙarshen wani taron bita na kwanaki uku da aka shirya wa daraktocin EFCC.
Ola Olukoyede ya danganta wannan nasara da sadaukarwa, ƙoƙari da jajircewar ma’aikatan hukumar, yana mai alƙawarin yin fiye da haka a shekarar 2025.
"A shekarar 2024, hukumar EFCC ta samu nasarori 4,111 a kotu tare da ƙwato kudade sama da N365.4 biliyan."
"Shugaban EFCC ya yaba da sadaukarwa, jajircewa, da ƙwarewar ma’aikatan hukumar, inda ya buƙaci ƙarin himma domin kafa sababbin tarihin nasara a 2025, tare da tabbatar da gaskiya da adalci a dukkan ayyuka."
- Dele Oyewale
Shugaban hukumar ya jaddada buƙatar tabbatar da ƙwarewa da gaskiya a yaƙi da cin hanci da rashawa, yana mai cewa ma’aikatan EFCC za su zama mutanen kirki masu ƙwazo da tasiri.
Ya kuma tabbatar da cewa cikin wata shida masu zuwa, zai kawo sabuwar EFCC a Najeriya.
Babban lauya ya yabawa hukumar EFCC
A nasa jawabin, babban lauya, Femi Falana (SAN), wanda ya yi bitar yadda EFCC ta samo asali, ya bayyana cewa hukumar ta zama abar alfahari kuma ba za ta gushe ba.
Ya jinjinawa Olukoyede da ɗaukacin ma’aikatan hukumar bisa jajircewa da kokarin da suke yi wajen yaki da cin hanci.
Femi Falana ya yi alƙawarin cewa za a yi bitar matsalolin da ke tattare da ɓangaren shari’a domin tabbatar da cewa hukumar ta cika burinta na magance cin hanci da rashawa a faɗin Najeriya.
EFCC ta cafke tsohon gwamnan Akwa Ibom
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta cafke tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Emmanuel Udom.
Hukumar EFCC ta cafke tsohon gwamnan ne kan zargin karkatar da N700bn daga asusun jihar a lokacin da yake kan kujerar mulki.
Jami'an na EFCC sun cafke Udom Emmanuel ne bayan wata ƙungiya ta shigar da ƙorafi kan yadda ya gudanar da dukiyar jihar a lokacin mulkinsa.
Asali: Legit.ng