Zargin Neman Lalata da Sanata Natasha: SERAP Ta Maka Shugaban Majalisa a Kotu

Zargin Neman Lalata da Sanata Natasha: SERAP Ta Maka Shugaban Majalisa a Kotu

  • Kungiyar SERAP ta maka shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio a kotu bisa dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan
  • SERAP ta ce dakatarwar wata shida ta tauye haƙƙin sanatar kuma ta hana al’ummar Kogi ta Tsakiya samun wakilci a majalisar dattawa
  • SERAP na neman kotu ta hana majalisa sake dakatar da Akpoti-Uduaghan, tana mai cewa matakin ya saɓa wa kundin tsarin mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyar SERAP ta maka shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, a kotu kan dakatarwar da ta kira “haramtacciya” da aka yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

An shigar da ƙarar ne a babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda SERAP ke neman a soke dakatarwar wata shida da aka yi wa sanatar bisa dalilin take hakkinta.

Kara karanta wannan

Natasha: Kungiyar 'yan majalisun duniya ta karbi koken Sanata, za ta ji ta bakin Akpabio

SERAP ta yi karar Akpabio kan dakatar da Sanata Natasha
SERAP ta maka Akpabio a kotu kan gaza janye dakatarwar da aka yiwa Sanata Natasha. Hoto: @NGRSenate
Asali: Twitter

SERAP ta maka Akpabio a kotu

A sanarwar da fitar a shafinta na intanet, kungiyar ta ce dakatarwar ta hana al’ummar mazabar Kogi ta Tsakiya wakilci a majalisa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka kuma, SERAP ta bayyana wannan ci gaban a cikin wata sanarwa da mataimakin daraktanta, Kolawole Oluwadare, ya rabawa manema labarai a ranar Lahadi.

A cewar SERAP, ƙarar da ta shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/498/2025 tana neman kotu ta tilasta wa Akpabio ya janye dakatarwar da gaggawa.

SERAP ta ga laifin majalisa kan dakatar da Natasha

Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha ne bisa zargin yin magana ba tare da izini ba da kuma ƙin amincewa da sabon wurin zama da aka bata.

Dakatarwar ta hana Sanata Natasha shiga harkokin majalisa, tare da dakatar da albashinta da duk wani alawus da take da haƙƙi a kansa.

Kara karanta wannan

Sanata Natasha ta kai karar Akpabio ga kungiyar 'yan majalisun duniya

SERAP ta yi watsi da wannan mataki, tana mai cewa babu wanda ya kamata a hukunta saboda yin magana ba tare da izini ba.

Kungiyar ta ce kasancewa sanata ba ya hana mutum samun haƙƙin bil'adama na asali da kundin tsarin mulki ya tanadar masa.

Ta jaddada cewa, kamata ya yi majalisar dattawa ta zama abin koyi wajen kare doka da haƙƙin ɗan adam, ba akasin hakan, ta hanyar take haƙƙinsu ba.

Rokon da SERAP ke yiwa kotu kan Akpabio

SERAP ta yi magana da ta yi karar Akpabio kan akatar da Sanata Natasha
SERAP ta shiga maganar dakatar da Natasha dumu-dumu, ta yi karar Sanata Akpabio. Hoto: @NGRSenate
Asali: Twitter

SERAP tana kuma neman kotu ta hana majalisar dattawa sake dakatar da Sanata Akpoti-Uduaghan saboda amfani da haƙƙinta na faɗin albarkacin baki.

Kungiyar ta yi nuni da cewa wannan dakatarwa ya ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya da yarjejeniyoyin kare haƙƙin ɗan adam na duniya.

SERAP ta bayyana cewa amfani da sashe na 6(1)(2) na dokokin majalisa wajen dakatar da Akpoti ya saɓa wa haƙƙin faɗin albarkacin baki.

Kara karanta wannan

Akpabio ya kalubalanci hurumin kotu kan koken Sanata Natasha

Ta ambato Sashe na 13 na Yarjejeniyar Kare Haƙƙin Mutane ta Afirka, wanda ke bai wa kowane ɗan ƙasa haƙƙin shiga harkokin mulkinsa.

An shigar da ƙarar ne a madadin SERAP ta hannun lauyoyinta, Kolawole Oluwadare da Mrs. Adelanke Aremo.

"Ba a sanya ranar sauraron ƙarar ba," in ji sanarwar.

Kwamitin majalisa ta gayaci Akpabio, Natsha

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kwamitin ladabtarwa da da'a na majalisar dattawa zai fara bincike kan zargin da ke kan shugaban majalisa, Godswill Akpabio, na neman lalata da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

Akpabio da Sanatar da ke wakiltar Kogi Ta Tsakiya za su gurfana gaban kwamitin domin yin bayani kan zargin cin zarafi da Natasha ta gabatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.