Bayan Sutale El Rufai, APC Ta Fadi Abin Koyi daga Muhammadu Buhari

Bayan Sutale El Rufai, APC Ta Fadi Abin Koyi daga Muhammadu Buhari

  • Jam'iyyar APC ta ji daɗin kalaman da Muhammadu Buhari ya yi kan tabbatar da ci gaba da zamansa mambanta
  • Mai magana da yawun jam'iyyar Felix Morka, ya yabawa tsohon shugaban ƙasan kam yadda ya nesanta kansa daga wasu ƴan siyasa
  • Ya buƙaci sauran mambobin jam'iyyar da su yi koyi da halin Buhari wajen nuna biyayya da sadaukarwa ga APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yabawa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Jam'iyyar APC ta yabawa Buhari ne bisa abin da ta kira kyakkyawan tabbacin biyayyarsa ga jam’iyyar.

APC ta yabawa Buhari
APC ta yabi Muhammadu Buhari Hoto: Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin jam'iyyar APC na ƙasa, Felix Morka, ya fitar a ranar Asabar a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buhari ya tabbatar da zamansa mamba a APC

A ranar 13 ga watan Maris, tsohon shugaban ƙasan ya bayyana cewa har yanzu yana nan a matsayin cikakken mamba na jam’iyyar mai mulki.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Shugaban jam'iyyar na kasa ya tsage gaskiya kan batun murabus

Buhari ya ce ba zai taɓa juya baya ga jam’iyyar da ta ba shi dama ya zama shugaban ƙasan Najeriya har sau biyu ba.

Wannan bayanin na sa ya zo ne sa’o’i bayan da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce ya tuntuɓi Buhari kafin ya yi murabus daga jam’iyyar APC.

A ranar 10 ga watan Maris, El-Rufai ya sanar da cewa ya koma jam’iyyar SDP bayan ya fice daga APC.

APC ta yabawa Buhari

A cikin sanarwar Felix Morka, ya jinjinawa tsohon shugaban ƙasan bisa nesanta kansa da ƙoƙarin wasu mutane da ke son danganta shi da zaɓin siyasar da suka yi cikin ruɗani.

Felix Morka ya ce tabbacin biyayyar Buhari ga jam’iyyar APC ya ƙara tabbatar da martabarsa a matsayin shugaba mai gaskiya da mutunci.

"Jam’iyyar APC na taya tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, murna da kuma yabawa bisa kyakkyawan tabbacin biyayyarsa ga jam’iyyarmu.”

Kara karanta wannan

Bayan El Rufai ya yi fatan ya dawo SDP, alamu sun nuna Peter Obi na shirin canza jam'iyya

"Muna jinjinawa tsohon shugaban ƙasan bisa yadda ya gaggauta bayyana matsayarsa tare da nisantar ƙoƙarin wasu da ke son danganta shi da zaɓin siyasar su da ba su da tabbas."
"Biyayyarsa maras yankewa ga jam’iyyarmu mai girma, wacce ta ba shi dama ya yi shugabanci a karo biyu, ta ƙara tabbatar da mutuncinsa da jajircewarsa a matsayin shugaba nagari da dattijo mai daraja.”
"Muna kira ga dukkan mambobin jam’iyyar mu da su kwaikwayi wannan kyakkyawan hali na Shugaba Buhari wajen nuna biyayya da sadaukarwa ga jam’iyyarmu mai girma."

- Felix Morka

An karrama Muhammadu Buhari

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata ƙungiya mai suna UFUK Dialogue ta karrama tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Ƙungiyar ta karrama Muhammadu Buhari ne ta hanyar ba shi lambar yabo ta zaman lafiya a yayin wani taron da ta gudanar.

Tsohon shugaban ƙasan ya yaba sosai kan lambar yabon da ya samu, musamman lura da cewa ya same ta ne bayan ya bar kan madafun iko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng