Rikicin PDP: Shugaban Jam'iyyar Na Kasa Ya Tsage Gaskiya kan Batun Murabus

Rikicin PDP: Shugaban Jam'iyyar Na Kasa Ya Tsage Gaskiya kan Batun Murabus

  • Muƙaddashin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya fito ya yi magana kan masu yaɗa cewa ya yi murabus
  • Umar Damagum ya bayyana rahotannin a.matsayin ƙarya da kuma aikin masu son kawo ruɗani a jam'iyyar
  • Ya buƙaci mambobin jam'iyyar da sauran masu ruwa da tsaki, su yi watsi da waɗannan rahotannin na ƙarya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Muƙaddashin shugaban Jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya yi magana kan batun cewa ya yi murabus daga muƙaminsa.

Umar Damagum ya musanta rahotannin da ke cewa ya yi murabus, yana mai bayyana su a matsayin ƙarya da aikin masu son tayar da fitina.

Damagum ya musanta yin murabus
Damagum ya musanta batun yin murabus daga shugabancin PDP Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Nuru Shehu Jos ya fitar a ranar Asabar, cewar rahoton jaridar Tribune.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe mahaddacin Kur'anin da suka sace a Katsina? An gano gaskiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me PDP ta ce kan murabus ɗin Damagum?

A cikin sanarwar, ya yi watsi da jita-jitar, yana mai bayyana ta a matsayin labari na bogi da aka yaɗa da gangan don yaudarar jama’a da haddasa rikici a cikin jam’iyya, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa Damagum bai sauka daga muƙaminsa ba, inda ta jaddada cewa kundin tsarin mulkin jam’iyyar yana bai wa shugabanta na ƙasa wa’adin shekara huɗu a karon farko.

"Hankalinmu ya kai ga wani rahoton ƙarya da ke iƙirarin cewa Umar Damagum ya yi murabus. Wannan ba komai ba ne illa labarin bogi da aka ƙirƙira don haddasa ruɗani."

Jam’iyyar ta kuma ƙaryata ikirarin da ke cewa Arise News ce tushen wannan rahoton ƙarya na murabus, tare da yin kira ga jama’a da su yi watsi da wannan labarin da ke neman yaudarar su.

PDP ta yi gargaɗi

PDP ta gargaɗi waɗanda ke yaɗa waɗannan rahotanni na ƙrya da su gaggauta dainawa, idan ba haka ba za su fuskanci fushin hukuma.

Kara karanta wannan

SDP ta tono 'makarkashiyar' da gwmanatin APC ke shiryawa El Rufai

"Muna jaddada cewa wannan labari na sharri da aka kirkira a kan Umar Damagum ƙarya ne, cin mutunci ne, kuma laifi ne. Doka za ta yi aiki kan waɗanda ke da hannu a wannan mummunan aiki ba da daɗewa ba."

Sanarwar ta buƙaci mambobin PDP, jiga-jigai, da magoya baya da su yi watsi da wannan labari na bogi, tare da tabbatar musu cewa jam’iyyar na nan daram kuma tana ci gaba da mayar da hankali kan ayyukanta.

"Muna kira ga dukkan mambobin PDP, dattawa, jiga-jigai, matasa, da ƙungiyoyin mata da su yi watsi da wannan labarin bogi kuma su ci gaba da kasancewa tsintsiya maɗaurinki ɗaya."
"Jam’iyyar na nan a tsaye daram a ƙarƙashin jagorancin Umar Damagum."

An fara lallashin Obi ya dawo PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP sun fara ƙoƙarin ganin Peter Obi ya dawo jam'iyyar.

Peter Obi wanda ya yi takarar shugaban ƙasa a 2023 a ƙarƙashin LP, ya fice daga PDP bayan zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2019.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng