Kalaman El Rufa'i Sun Tada Ƙura, Ƴan Sanda Sun Yi Magana kan Zargin 'Sace Kwamishina'

Kalaman El Rufa'i Sun Tada Ƙura, Ƴan Sanda Sun Yi Magana kan Zargin 'Sace Kwamishina'

  • Rundunar ƴan sandan Kaduna ta musanta zargin da Nasir El-Rufai ya yi cewa dakarunsa sun sace tsohon kwamishina saboda ya bar APC
  • Kakakin ƴan sandan, DSP Mansir Hassan ya ce zargin ba gaskiya ba ne domin babu masu garkuwa da mutane a cikin rundunar ƴan sanda
  • El-Rufai dai ya yi zargin cewa tawagar masu garkuwa da ke biyayya ga Uba Sani ne suka cafke abokinsa kuma tsohon kwamishina a gwamnatinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Rundunar ‘yan sandan Kaduna ta yi martani kan zargin da tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, ya yi cewa an sace tsohon kwamishinansa, Mallam Jafaru Sani.

El-Rufai ya sake yamutsa hazo a Kaduna yayin da ya zargi ƴan sanda da yin garkuwa da Mallam Jafaru Sani da sunan bincike.

Yan sanda da El-Rufai.
Yan sanda sun maidawa El-Rufai martani kan zargin sace tsohon kwamishina Hoto: Nigeria Police Force, Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

Wane zargi El-Rufai ya yi wa ƴan sanda?

Kara karanta wannan

Tsofaffin ministocin Buhari 10 da manyan ƙusoshi na shirin bin El Rufai zuwa SDP

Nasiru El-Rufai, wanda ya mulki Kaduna daga 2015 zuwa 2023, ya bayyana a shafinsa na X cewa Jafaru Sani ya shiga matsi saboda ya fice daga jam’iyyar APC zuwa SDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

"Tawagar masu garkuwa na Uba Sani da ke iƙirarin cewa su ƴan sanda ne sun sace abokinmu kuma tsohon kwamishina a gwamnatinmu, Mallam Jafaru Sani a Kaduna da rana tsaka.
"Kotun majistar ta tsare shi a gidan yari ba tare da rahoton binciken farko daga ‘yan sanda ko tuhume-tuhume daga Ma’aikatar Shari’a ta Jihar ba."

Yan sanda sun maidawa El-Rufai martani

A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya fitar a ranar Juma’a, ya musanta wannan zargi, rahoton Daily Trust.

Sanarwar ta ce:

"An ja hankalin rundunar ƴan sandan Kaduna kan wani zargi da tsohon gwamna, Malam Nasir El-Rufai ya yi cewa an yi garkuwa da tsohon kwamishinansa, Malam Jafaru Sani."

Kara karanta wannan

"Ba mu yarda ba," El Rufai ya ƙara shiga matsala bayan komawa SDP, matasa sun masa rubdugu

"Ku sani babu masu garkuwa da mutane a cikin rundunar ‘yan sanda ta Najeriya. A matsayinta na hukuma da ke ƙarƙashin kundin tsarin mulkin 1999, ‘yan sanda na da alhakin tabbatar da doka da oda."
"Duk wanda ake zargi da aikata laifi, ‘yan sanda na da hurumin kama shi, gudanar da bincike, da gurfanar da shi a kotu."
Jami'an yan sanda.
Yan sanda sun musanta zargin El-Rufai, sun ce kundin tsarin mulki ya ba su damar kama wanda ake zargi Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Ƴan sanda sun gargaɗi shuwagabanni

Rundunar ta kuma yi kira ga tsofaffin shugabanni da su guji yin zarge-zargen da ba su da tushe, yana mai cewa irin wadannan maganganu kan haifar da rudani da matsalar tsaro.

"Idan wani yana jin an ci zarafinsa, ya bi hanyar shari’a maimakon yin maganganu masu tayar da fitina da ka iya haifar da tashin hankali."

Ana ganin dai wannan lamari na kara rura wutar rikicin siyasa tsakanin El-Rufai da magajinsa, Malam Uba Sani a Kaduna.

Matasan SDP sun yi watsi da El-Rufai

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Tsohon gwamna El-Rufai ya zargi 'yan sanda da 'sace kwamishina'

A wani labarin, kun ji cewa matasan SDP sun yi zargin cewa ba don Allah Malam Nasir El-Rufai ya shiga jam'iyyarsu ba sai don cimma burinsa.

A cewar shugaban ƙungiyar matasan SDP, Kwamared Abdulsamad Bello, El-Rufai bai cancanci shiga SDP ba ta kowace fuska.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng