"Mutane Miliyan 1 Za Su Samu": Ɗangote Ya Fara Raba Tallafin Naira Biliyan 16 ga Ƴan Najeriya

"Mutane Miliyan 1 Za Su Samu": Ɗangote Ya Fara Raba Tallafin Naira Biliyan 16 ga Ƴan Najeriya

  • Gidauniyar hamshaƙin attajirin nan, Alhaji Aliko Ɗangote ta fara rabon kayaan abinci na kimanin Naira biliyan 16 a Najeriya
  • An ruwaito cewa aƙalla mutane marasa galihu miliyan ɗaya ne za su amfana da tallafin Ɗangote a faɗin kananan hukumomi 774
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya yabawa Ɗangote bisa yadda ya himmatu wajen yaƙi da yunwa da fatara a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Gidauniyar Aliko Dangote (ADF) ta kaddamar da shirin tallafin abinci na ƙasa na 2025 a ranar Alhamis, ana sa ran ƴan Najeriya miliyan ɗaya za su amfana.

Tallafin da gidauniyar attajirin za ta rabawa mutane mabukata zai laƙume kudi Naira biliyan 16 a faɗin jihohi 36 da Abuja.

Dangote ya fara rabon shinkafa.
Dangote ya kaddamar da fara rabon buhunan shinkafa ga marasa galihu a jihar Kano Hoto: @SasDantata
Asali: Twitter

Ɗangote ya fara raba buhunan shinkafa

Tribune Nigeria ta ce a karkashin shirin, fiye da 'yan Najeriya miliyan daya, kowanensu zai karɓi buhun shinkafa mai nauyin kilo 10.

Kara karanta wannan

Yunkurin tsige gwamna ya jefa Shugaba Tinubu a matsala, an yi masa barazana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan tallafi zai taimaka wajen rage matsin tattalin arziki da rage yunwa a faɗin ƙasar nan musamman a wannan wata na Ramadan.

A lokacin kaddamar da shirin a Kano, shugaban gidauniyar, Alhaji Aliko Dangote, wanda ‘yarsa Mariya Aliko Dangote ta wakilta, ya ce rabon buhunan shinkafar na cikin tsare-tsarensa na tallafawa marasa galihu.

Ya ce wannan tallafi za a raba shi ne ga mutane marasa galihu akalla miliyan ɗaya a faɗin kananan hukumomi 774.

An fara rabon tallafin a jihar Kano

Dangote ya ƙara da cewa an fara rabon abincin ne a jihar Kano, daga nan kuma za a ci gaba da rabawa a sauran jihohi, domin tabbatar da cewa abincin ya kai ga waɗanda suka fi buƙata.

Ya ce gidauniyar tana aiki tare da gwamnatocin jihohi domin tabbatar da cewa tallafin ya isa ga marasa galihu a duk faɗin ƙasar.

Hamshakin ɗan kasuwar ya ce:

Kara karanta wannan

Al-Mustapha ya ziyarci Atiku awanni da sauya sheka zuwa jam'iyyar SDP

"Abinci yana da matukar muhimmanci ga rayuwar dan Adam. Saboda haka, mun ga dacewar aiwatar da wannan shiri domin rage radadin yunwa a tsakanin jama'a."

Ɗangote ya bukaci ƴan kasuwa su taimaka

Ɗangote, ya kuma yi kira ga manyan ‘yan kasuwa da kamfanoni masu zaman kansu da su taimaka wajen tallafawa marasa galihu.

Leadership ta rahoto Ɗangote na cewa:

"Wannan aiki ba na gwamnati kaɗai ba ne. Muna buƙatar haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da ‘yan kasuwa domin magance matsalar yunwa.
"Ina gode wa gwamnatoci a matakai daban-daban bisa ƙoƙarinsu na magance matsalar karancin abinci. Da haɗin kai, za mu shawo kan wadannan ƙalubale."
Dangote.
Dangote ya fara raba kayan abinci karƙashin gidauniyarsa Hoto: Aliko Dangote
Asali: Getty Images

Gwamna Abba ya yabi Aliko Ɗangote

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda mataimakinsa Comrade Aminu Abdulsalam Gwarzo ya wakilta, ya ce shirin na nuna jajircewar Aliko Dangote wajen yaki da yunwa da talauci a Najeriya.

A cewarsa, buhuna 120,000 na shinkafa za a raba a faɗin ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano.

Kara karanta wannan

2027: Yan adawa na shirin firgita Tinubu, ƙusa a PDP ya ce guguwar canji za ta tafi da APC

Aminu Abdulsalam Gwarzo ya jinjinawa Alhaji Aliko Dangote, yana mai cewa:

"A shekarar da ta gabata ma an gudanar da irin wannan rabon kayan abinci, wanda ya amfanar da marasa galihu da dama."

Ɗangote ya kara rage farashin fetur

A wani rahoton, kun ji cewa Ɗangote ya sake rage farashin kowace litar man fetur daga N825 zuwa N815 domin saukakawa ƴan Najeriya.

‘Yan kasuwa sun ji daɗin rage farashin, kuma tuni suka fara siyan man kai tsaye daga matatar Dangote maimakon daga hannun masu ajiyar man da ke zaman kansu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen hausa na legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng