Jami'an Tsaron Kano Sun Dira kan masu Kunnen Kashi, An Cafke Matasa 28

Jami'an Tsaron Kano Sun Dira kan masu Kunnen Kashi, An Cafke Matasa 28

  • Kwamitin tsaron hadin gwiwa na jihar Kano ya kama mutum 28 da ake zargi da aikata ayyukan daba a sassa daban-daban
  • An gudanar da kamen ne a mabanbantan lokuta a tsakanin 3 zuwa 13 ga watan Maris, 2025, bayan rahotannin sirri da aka samu
  • Ana zargin matasan da karya doka, musamman a lokacin azumin Ramadan tare da yunkurin ayyukan tayar da zaune tsaye

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KanoKwamitin hadin gwiwar tsaro ta jihar Kano ta kama wasu mutum 28 da ake zargi da shirin aikata ayyukan ta’addanci da tada zaune tsaye.

A cewar kakakin kwamitin, wanda kuma shi ne Kwamishinan yada labarai na Kano, Ibrahim Waiya, an kama mutanen ne tsakanin 3 zuwa 13 ga watan Maris, 2025.

Kara karanta wannan

Kano: Fashewar tukunyar gas ta jawo asarar rai, ƴan sanda sun ɗauki matakin gaggawa

Gwamnati
Kwamitin tsaron gwamnatin Kano ya kama matasa 28 Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa an cafke su ne a yayin da ake gudanar da samame na musamman don raba jihar Kano da ɓata gari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kai samamen zuwa muhimman wurare a cikin birnin Kano, bayan samun rahotannin sirri cewa ana shirin aikata ayyukan ta’addanci a cikin watan azumi.

An kwace miyagun makamai a jihar Kano

Jaridar Leadership ta wallafa cewa kwamitin tsaron hadin gwiwar, Kano ya hada da ‘yan sanda, DSS, NDLEA, NSCDC, jami’an gidan gyaran hali, da kungiyar bijilanti.

Jihar
Gwamnatin Kano ta yi alkawarin kakkabe rashin tsaro Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jami'an kwamitin sun yi nasarar kwace wasu kayayyaki masu hadari, da suka hada da: fakiti 283 na ganyen da ake zargin tabar wiwi ce, da takubba.

Haka kuma ƙwace almakashi uku, wani karfe mai kaifi, kwalabe biyu na sukudayin da sauran miyagun kayayyakin da za su firgita jama'a.

Kano ta maka magana a gaban kotu

Kwamishinan ya bayyana cewa an gurfanar da wadanda ake zargin a kotun Majistare mai lamba 12 da ke filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano domin fuskantar shari’a. Ya nanata cewa gwamnatin Kano ta haramta tashe ne a bana domin tabbatar da zaman lafiya a watan Ramadan, ganin yadda ya ne da alaka da tayar da hatsaniya.

Kara karanta wannan

Saukaka sufuri: Za a samar da motoci masu aiki da lantarki 10,000 a Arewa

Gwamnatin ta jaddada cewa ba za ta lamunci matasa su rika tayar da hankulan jama'a a lokacin da musulmi ke ibadar azumi Ramadana ba.

Gwamnatin Kano ta nemi haɗin kai

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta bukaci hadin kan jama’a wajen tabbatar da tsaro da inganta rayuwar mazauna dukkanin sassan jihar Kano.

Shugaban kwamitin hadin gwiwar tsaron, Yusuf Kofar mata, ya jinjinawa jami’an tsaro da suka gudanar da aikin, tare da fatan za a ci gaba da samun hadin kan jama'a.

An tura sabon Kwamishinan ƴan sanda Kano

A baya, kun samu labarin cewa hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda (PSC) ta amince da nadin CP Ibrahim Adamu Bakori a matsayin sabon kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano.

CP Ibrahim Bakori, wanda ya fito daga jihar Katsina, ya maye gurbin tsohon kwamishinan ‘yan sanda na Kano, Salman Garba Dogo, wanda aka kara wa girma zuwa mukamin AIG.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.