Farashin Man Fetur Ya Kama Hanyar Ƙara Araha, Sauƙi Zai Lulluɓe Yan Najeriya
- Ana hasashen farashin man fetur ka iya ƙara sauka a Najeriya idan farashin gangar mai a kasuwannin duniya ya ci gaba da faɗuwa
- Rahoto ya nuna gangar ɗanyen mai ta yi saukar da ba ta taɓa yi ba a makonni da dama da suka gabata, wanda ya sa ake ganin sauƙi na tafe
- Wani masanin tattalin arziki, Paul Alaje ya ce duba da abin da ke faruwa a kasuwannin duniya, kowace lita na iya dawowa N700
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Farashin man fetur (PMS) na iya ci gaba da saukowa a Najeriya idan kudin danyen mai ya ci gaba da yin kasa a kasuwannin duniya.
Wannan hasashen dai na zuwa ne da kamfanin mai na ƙasa (NNPCL) da matatar Ɗangote suka rage farashin litar fetur kusan ana gab da fara azumin Ramadan.

Asali: Original
Rahoton Punch ya bayyana cewa hakan na da alaka da yadda darajar Naira ke ƙara farfaɗowa a kasuwar hada-hadar kudin ketare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda farashin gangar mai ya faɗi
A wannan mako, farashin danyen mai ya fadi da kusan kashi 2%, wanda hakan ya sa ya yi faɗuwa mafi kasa cikin makonni 12.
Farashin gangar mai ta Brent ya ragu da dala 1.19 ko kuma kashi 1.6%, inda kowace ganga guda ta sauka zuwa dala 71.62.
Haka kuma, farashin gangar mai ta West Texas Intermediate (WTI) ya ragu da dala 1.39 ko kuma kashi 2%, ya ruguzo zuwa dala 68.37 kowace ganga.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa wannan shi ne mafi karancin farashi da Brent ya kai tun ranar 6 ga Disamba, haka ma WTI tun 9 ga Disamba.
Dalilin faɗuwar farashin ɗanyen mai
An danganta raguwar farashin ne da matakin da ƙungiyar OPEC+ (wadda ke haɗa kasashen OPEC da abokan hulɗarta kamar Rasha) ta ɗauka, na ci gaba da ƙara yawan danyen mai da ake fitarwa daga watan Afrilu.
Masana a bangaren kasuwancin man fetur a Najeriya sun ce farashin danyen mai da kuma darajar Naira a kasuwar hada-hadar kudi su ne manyan abubuwan da ke ƙayyade kudin fetur.
A makon da ya gabata, matatar man Dangote ta rage farashin man fetur daga N890 zuwa N825 kowacce lita.
Kamfanin NNPCL ya bi sahu, ya daidaita farashinsa da na Dangote, wanda hakan ya janyo abinda wasu ke kira “gasa a farashin man fetur.”

Asali: Twitter
Masana sun hango raguwar farashin fetur
Wani masanin tattalin arziki, Paul Alaje, ya bayyana cewa wannan raguwar farashi za ta iya dorewa.
A cewarsa, yana ganin farashin man fetur zai iya faɗuwa ƙasa, kowace lita ta dawo N700 idan aka yi la’akari da halin da ake ciki a kasuwannin duniya.
A wata hira da Channels tv, Alaje ya ce:
“Idan har farashin danyen mai bai kara tashi ba sakamakon wata matsala ta duniya, to da yiwuwar a rage farashin man fetur zuwa N700 kowacce lita."
Shugaban kungiyar masu sayar da man fetur a Najeriya (PETROAN), Billy Gillis-Harry ya yi magana game da lamarin.
'Dan kasuwar ya ce farashin fetur zai ci gaba da sauyawa daidai da yadda kudin danyen mai ke tafiya a kasuwannin duniya.
Kudin sufuri ba ya raguwa
Wani ɗan kasuwa, Abba Kabir mai hatsi ya shaidawa Legit Hausa cewa saukar fetur da kayan abinci abin farin ciki ne domin zai sauƙaƙawa mutane matsin da suke ciki.
Sai dai kasancewarsa mai yawan tafiye-tafiye saboda kasuwancinaa, ya ce yana mamakin yadda masu motocin haya suka ƙi rage kuɗin sufuri.
Abba ya zargi wasu mutanen da laifin duk abin da ke faruwa, yana mai cewa galibin masu zagin shugabanni idan suka samu dama ɓarnar da za su tana da yawa.
"Muna fatan mai ya ci gaba da sauka, ko bakomai kayan abinci suna sauka a kasuwanni, amma abin da ke bani mamaki shi ne kuɗin sufuri.
"Mutanenmu suna kuka da babu amma sun san su kara kuɗi idan mai ya tashi, idan ya sauka kuma ba za su rage komai ba, da an yi magana ka ji suna ai dama haƙuri kawai su ke." in ji shi.
Ya buƙaci direbobin motocin haya su ji tsoron Allah su rage farashin sufuri kamar yadda suka samu sauki wajen sayen man fetur.
PETROAN ta ji daɗin rage litar fetur
A wani labarin, kun ji cewa ƙungiyar dillalan man fetur ta Najeriya (PETROAN) ta yi farin ciki da rage farashin litar mai a Najeirya, ta ce hakan zai sauƙaƙawa mutane.
Shugaban PETROAN, Dr. Billy Gillis Harry ya ce rage farashin fetur zai taimaka wajen rage tsadar sufuri, wanda hakan zai haifar da sauƙi a rayuwar ‘yan Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng