Abin da Dillalai Suka Hango bayan NNPCL da Matatar Ɗangote Sun Rage Farashin Fetur
- Saukin da aka samu kwanan nan a farashin man fetur a Najeriya ya yi wa ƙungiyar daillalan mai ta ƙasa watau PETROAN daɗi
- Matatar Ɗangote da kamfanin mai na kasa watau NNPCL sun rage farashin man lokacin da al'ummar musulmin ƙasar suka fara azumi
- Shugaban PETROAN na ƙasa, Dr. Billy Gillis Harry ya ce sauke farashin zai rage wa ƴan Najeriya radaɗin tsadar rayuwar da suke fuskanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ƙungiyar dillalan man fetur ta Najeriya (PETROAN) ta yi farin ciki da rage farashin litar mai a Najeirya, tana mai cewa hakan zai rage wa mutane raɗaɗi.
Kungiyar PETROAN ta jinjinawa kamfanin mai na ƙasa watau NNPCL saboda rage farashin man fetur (PMS) daga N920 zuwa N875 kowace lita.

Asali: Twitter
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da shugaban PETROAN, Dr. Billy Gillis Harry, ya fitar, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan
"Ku bi a hankali," Omokri ya bukaci CAN ta guji shari’a da jihohi kan hutun Ramadan
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa wannan mataki zai rage wa ‘yan Najeriya raɗaɗin tsadar rayuwa, musamman a daidai lokacin da hauhawar farashi ke ƙaruwa a ƙasar.
Rage tsadar fetur zai saukakawa mutane
Dr. Billy Gillis Harry ya ce rage farashin fetur zai taimaka wajen rage tsadar sufuri, wanda hakan zai haifar da sauƙi a rayuwar ‘yan Najeriya.
"Idan an rage farashin fetur, farashin sufuri zai ragu, hakan zai sauƙaƙa wa mutane zirga-zirga da safarar kayayyaki.
"Haka nan kuma rage farashin fetur zai kawo saukar farashin abinci saboda sauƙin safarar kaya," in ji shi.
PETROAN ta yabawa matatar Ɗangote
Gillis Harr ya kuma yabawa matatar Dangote bisa yadda ta maida wa masu gidajen mai N65 a kowace lita sakamakon asarar da suka yi saboda rage farashin fetur, in ji Punch.
Ƙungiyar PETROAN ta bayyana cewa matatar Alhaji Aliko Dangote ta yanke shawarar rage farashin kowace litar man fetur daga N890 zuwa N825.

Kara karanta wannan
Ramadan: Ɗan Shugaba Bola Tinubu ya yamutsa siyasar Kano a wurin buɗa bakin azumi
"Har ila yau, matatar ta amince tare da maida wa masu gidajen mai N65 a kowace lita daga cikin litar fetur tan miliyan 200 da suka riga suka saya kafin a rage farashin."
Ɗangote ya yi abin a yaba masa
PETROAN ta ce wannan mataki zai taimaka wajen rage hasarar masu gidajen mai, tare da tabbatar da adalci ga ‘yan kasuwa da masu amfani da fetur a ƙasar.
"Matatar Dangote ta amince da asarar N16bn don biyan waɗanda suka sayi fetur a tsohon farashi.
"Wannan ya nuna cewa matatar ta na da kishin abokan kasuwancinta da kuma walwalar masu amfani da fetur,"
- Dr. Billy Gillis-Harry.
Ya ƙara da cewa kungiyar PETROAN na goyon bayan wannan yunƙuri, kuma ta buƙaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da kyautata zato kan sauye-sauyen da gwamnati ke yi domin inganta rayuwar al’umma.
MRS ya rage farashin fetur a gidajen mai

Kara karanta wannan
Shugaba Tinubu ya amince da kafa sababbin Jami'o'i 11 a Najeriya, an jero sunayensu
A wani labarin, kun ji cewa Kamfanin makamashi na MRS ya rage farashin litar fetur a gidajen mansa bayan matatar Ɗangote ta sanar da sabon farashi.
Ana ganin ragin farashin na cikin kokarin rage radadin hauhawar farashin kaya, wanda zai taimaka wajen rage matsin rayuwar da ake fuskanta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng