Rikicin Sarauta Ya Ƙara Tsanani, Sarki Ya Yi Sabon Naɗin da Zai Iya Tayar da Ƙura
- Mai martaba sarkin Wase da ke jihar Filato, Alhaji Muhammad Sambo Haruna ya naɗa sabon waziri duk da rikicin sarautar da ke gaban kotu
- Rahotanni sun nuna cewa sarkin Wase da tsohon wazirinsa ba su ga maciji kuma har lamarin ya kai ga shiga kotu duk da koƙarin sulhun da aka yi
- Wata majiya daga gidan sarautar ta bayyana cewa an yi duk abin da ya kamata domin sasanta rikicin a jihar Filato amma abin ya ci tura
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Plateau - Rikicin sarautar wazirin masarautar Wase da ke ƙaramar hukumar Wase a jihar Filato ya kara ɗaukar zafi a baya-bayan nan.
Rahotanni sun nuna cewa an naɗa Injiniya Abubakar Abubakar, tsohon babban sakatare a ma’aikatar albarkatun ƙasa a matsayin sabon Waziri na Wase.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa an gudanar da bikin naɗin sabon wazirin ne a ranar Jumma’a, 7 ga watan Maris, 2025.

Kara karanta wannan
Gwamna ya ƙara shiga tsaka mai wuya, Majalisar Dokoki ta dawo da shirin tsige shi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarkin Wase ya naɗa sabon waziri
An tattaro cewa an naɗawa wazirin rawani duk da wata shari’a da ke gudana tsakanin Mai Martaba Sarkin Wase, Alhaji Muhammad Sambo Haruna, da tsohon Wazirin Wase, Alhaji Muhammadu Badamasi a kotu.
Wannan al'amari dai ya haddasa rikici mai tsanani tsakanin sarakunan biyu, wanda a yanzu ya buɗe sabon shafi bayan sarki ya naɗa sabon waziri.
Yadda alaƙa ta yi tsami tsakaninsu sarki da waziri
An ruwaito cewa dangantaka tsakanin Mai Martaba Sarkin Wase da tsohon wazirin nasa ta yi tsami, har ta kai ga shiga kotu.
An tuhumi tsohon waziri da laifin cin zarafin Sarki da kuma ƙoƙarin tayar da zaune tsaye a cikin garin Wase. Sai dai ya musanta waɗannan zarge-zarge.
Ƙoƙarin sulhu tsakaninsu ya ci tura
Majiyoyi daga yankin masarautar sun bayyana cewa an yi ƙoƙarin sulhunta sarkin Wase da tsohon wazirin amma hakan bai yiwu ba domin duk wani yunkuri bai kai wa ga nasara.
Wata majiya ta ce dangin masarauta sun yi iyakar ƙoƙarinsu don sasanta rikicin kafin daga bisani su yanke shawarar naɗa sabon waziri.
Duk wani yunkuri na sasanta su ya ci tura domin tsohon Waziri ya nace cewa ba zai ci gaba da aiki a ƙarƙashin Sarki Alhaji Muhammad Sambo Haruna ba.
An shirya fara sauraron shari’ar a ranar 28 ga Fabrairu, amma daga baya Kwamishinan Shari’a na Jihar Filato, Philemon Dafi, ya ɗauki nauyin jagorantar shari’ar.
A halin yanzu dai mutanen yankin Wase za su saurari yadda za ta kaya a gaban alkali domin kawo karshen wannan taƙaddama da ta ƙi ci kuma ta ƙi cinye wa.
Gwamna Makinde ya dawo da sarki kan sarauta
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya maido da sarkin Eruwa da ke ƙaramar hukumar Ibarapa ta Gabas.
Gwamnan ya dawo da basaraken kan karagar mulki ne bayan kusan shekaru biyar da kotun Najeriya ta tsige shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng