An Kama Babban 'Dan Bindiga da Ya Tara Miliyoyin Naira a Daji

An Kama Babban 'Dan Bindiga da Ya Tara Miliyoyin Naira a Daji

  • 'Yan sanda sun tarwatsa wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane da ke addabar yankunan Ikot Ekpene da Essien Udim a Akwa Ibom
  • A yayin samamen, an kashe mutum guda daga cikin miyagun, an kama wasu, tare da kwace makamai da miliyoyin kuɗi a hannunsu
  • Rundunar ‘yan sandan Akwa Ibom ta yi alƙawarin ci gaba da aikin kawar da ‘yan ta’adda masu garkuwa da mutane da sauran laifuffuka

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum

Akwa Ibom - Rundunar ‘yan sanda a jihar Akwa Ibom ta samu gagarumar nasara bayan ta tarwatsa wata fitacciyar ƙungiyar masu garkuwa da mutane.

A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Timfon John, jami’an tsaro sun kai samame maboyar ‘yan ta’addan ne inda suka yi nasarar kwato manyan makamai da kuɗi masu yawa.

Kara karanta wannan

Yaki da 'yan bindiga: Jami'an sojoji sun kashe 'Gwamna' a jihar Katsina

Yan sanda
'Yan sanda sun tarwatsa 'yan bindiga a Akwa Ibom. Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Punch ta wallafa cewa ‘yan sanda sun bayyana cewa wannan aiki wani bangare ne na kokarinsu na tabbatar da tsaro a jihar Akwa Ibom.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka tarwatsa masu garkuwa

Kakakin 'yan sanda, DSP Timfon John ta bayyana cewa jami’an tsaro sun samu sahihan bayanan sirri kafin kai harin.

A cewar DSP Timfon John:

“Ƙungiyar haɗin guiwa ta jami’an tsaro ta kai samame a maboyar ‘yan ta’addan da ke Ikpe Annang, Ikpe Ikot Akpan, da Ikot Inyang a ƙaramar hukumar Essien Udim.”

A lokacin da jami’an tsaro suka kai farmaki, ‘yan bindigar sun yi ƙoƙarin tserewa ta hanyar buɗe wuta, amma jami’an tsaro sun mayar da martani.

A faɗar DSP John:

“Da ‘yan ta’addan suka hango jami’an tsaro, suka buɗe musu wuta domin tserewa, amma jami’anmu suka mayar da martani.”

A yayin gumurzun, an ji wa ‘yan ta’adda biyar raunuka, aka garzaya da su asibiti, amma ɗaya daga cikinsu ya rasu.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kutsa cikin gida a Kano, sun yi ta'asa bayan cirewa wani ƴan yatsu

An kwato makamai da kuɗi masu yawa

Bayan an kammala farmakin, jami’an tsaro sun samu nasarar kwace makamai da dama daga hannun ‘yan bindigar.

DSP John ta bayyana cewa:

“Mun samu bindiga kirar AK-47, bindigar G3, da wata bindigar gargajiya.”

Baya ga hakan, an kwato wasu kayayyaki kamar jaka cike da ƙifi, ƙararrawa, wata na’urar ƙara amo da gangar rawa.

Haka kuma, jami’an tsaro da suka kai farmakin sun samu tsabar kuɗi sama da Naira miliyan 3 a maboyar ‘yan ta’addan.

Rundunar ‘yan sanda ta yi gargadi

Bayan wannan nasara, kwamishinan ‘yan sandan jihar Akwa Ibom, Baba Azare, ya jinjinawa jami’an tsaro bisa kwazon da suka nuna.

Ya kuma gargadi sauran ‘yan ta’adda da ke addabar jihar da cewa ba za su tsira daga hukuncin doka ba.

A cewarsa:

Kara karanta wannan

Bayan alkawarin gwamna kan miyagu, jami'an tsaro sun hallaka jagoran Lakurawa

“Jihar Akwa Ibom ba za ta ƙara zama mafakar ‘yan ta’adda ba. Za mu ci gaba da farautarsu har sai mun kawar da su gaba ɗaya.”

Kwamishinan ya kuma bukaci hadin gwiwar jama’a da jami’an tsaro domin hana ayyukan ta’addanci a jihar.

Yan sanda
Sufeton 'yan sandan Najeriya. Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

An kashe dan bindiga Gwamna a Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojin Najeriya sun kai gagarumin farmaki kan 'yan bindiga a jihar Katsina.

Rahotanni sun nuna cewa an samu nasarar kashe wani jagoran 'yan bindiga mai suna Yusuf Gwamna tare da jikkata wasu da dama.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Ibrahim Yusuf, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng