Tinubu Ya Fadi abin da ba a Yi Zato ba kan Osinbajo bayan Zaben Fitar da Gwani a 2023

Tinubu Ya Fadi abin da ba a Yi Zato ba kan Osinbajo bayan Zaben Fitar da Gwani a 2023

  • Shugaba Bola Tinubu ya taya tsohon mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, murnar cikarsa shekaru 68, yana yabonsa bisa kokarinsa ga kasa
  • Tinubu ya jaddada rawar da Osinbajo ya taka wajen gudanar da gwamnati da ayyukan ci gaba lokacin da yake mataimakin Shugaba Muhammadu Buhari
  • Ya kuma tuna yadda Osinbajo ya nuna kwarewarsa a lokacin da ya zama mukaddashin shugaban kasa yayin da Buhari ke jinya a Birtaniya
  • Tinubu ya bayyana cewa Osinbajo yana da 'yancin takara a APC kan zaben fitar da gwani a 2023, kuma har yanzu aboki ne a tafiyar siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo murnar zagayowar ranar haihuwarsa ta shekaru 68.

Tinubu ya taya Osinbajo murna inda ya jero gudunmawar da ya ba Najeriya musamman lokacin da yake mataimakin shugaban kasa a mulkin Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Tinubu ya gwangwaje Farfesa Jega da babban mukami a gwamnatinsa

Tinubu ya taya Osinbajo murnar cika shekaru 68
Bola Tinubu ya yi addu'o'i da fatan alheri ga Yemi Osinbajo. Hoto: Bayo Onanuga.
Asali: Facebook

Tinubu ya jero gudunmawar da Osinbajo ya bayar

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Dada Olusegun ya wallafa a shafin X a jiya Asabar 9 ga watan Maris din 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Osinbajo, wanda ya kasance mataimakin shugaban kasa daga 2015 zuwa 2023, ya samu yabo daga Tinubu saboda gudunmawarsa ga cigaban kasa.

Tinubu, a cikin wata sanarwar ya jaddada irin nasarorin Osinbajo wajen gudanar da gwamnati da ayyukan alheri ga kasa.

Shugaban ya kuma tuna da lokacin da Osinbajo ya jagoranci kasa a matsayin mukaddashin shugaban kasa yayin da Buhari ke jinya a Landan.

Tinubu ya kara da yabawa aikin Osinbajo a matsayin Kwamishinan Shari'a lokacin gwamnatinsa a Legas, inda suka yi hadin gwiwa wajen kawo sauye-sauye.

Tinubu ya fadi gudunmawar da Osinbajo ya bayar a Najeriya
Bola Tinubu ya raya Farfesa Yemi Osinbajo murnar cika shekaru 68 a duniya. Hoto: @DOlusegun.
Asali: Twitter

Tinubu ya magantu bayan takararsa da Osinbajo

Tinubu ya ce Osinbajo ya yi amfani da ‘yancinsa na dimokuradiyya wajen tsayawa takarar tikitin shugaban kasa na APC a 2023 wanda shugaban ya yi nasara.

Kara karanta wannan

Da gaske ne Atiku ya sauya sheka, zai yi takarar 2027 a SDP?

Ya ce:

“Farfesa Osinbajo ya yi amfani da ‘yancinsa na dimokuradiyya da ‘yancin walwala a shekarar 2023 lokacin da ya tsaya takarar tikitin shugaban kasa na jam’iyyar APC tare da ni.”
“Farfesa Yemi Osinbajo zai ci gaba da kasancewa abokina kuma abokin tafiya, ya yi wa kasar nan aiki tukuru a matsayin mataimakin shugaba.”
“Ya sa dukkanmu a jam’iyyar APC alfahari, ta hanyar aiki da Buhari cikin hadin kai ba tare da sun samu wani sabani ba."

Shugaban ya hada da iyalan Osinbajo, matarsa Dolapo da ’ya’yansa da abokai, inda ya yi musu fatan karin lafiya, nasara da daukaka.

Hadimin Osinbajo ya caccaki salon mulkin Tinubu

A baya, kun ji cewa tsohon hadimin shugaban kasa, Babafemi Ojudu, ya ce Bola Tinubu bai dace ya jagorancin Najeriya a wannan lokaci ba.

Dan siyasar ya bayyana cewa Farfesa Yemi Osinbajo zai iya jagorantar Najeriya da basira da hangen nesa fiye da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Ojudu ya ce manufofin Tinubu ba su dace da Najeriya a wannan lokaci ba, yana mai nuna rashin gamsuwarsa dangane da tsare-tsaren gwamnatin da ke jefa al'umma cikin mummunan yanayi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.