Malaman cocin Katolika na Najeriya sun bukaci shugaba Buhari ya sauka daga mulki

Malaman cocin Katolika na Najeriya sun bukaci shugaba Buhari ya sauka daga mulki

- A kisan da ake ta fama dashi wanda Filani keyi a fadin kasar nan wanda ya hada da wasu malaman kirista guda biyu da akashe da kuma wasu mutane 15 a jihar Binuwai, manyan malaman kirista na Najeriya sunyi kira da shugaba Buhari akan ya sauka daga mulki

- CBCN sun bukaci shugaba Buhari ya daina wasu shawarwari game da yawan kisa da akeyi a fadin kasar, kawai ya sauka daga kan mulki kafin kasar ta ida rushewa baki daya

- Shugaban malaman Rev. Augustine Akubeze da sakataren malaman Rev. Camillus Umoh, suka bayyana kiran wanda malaman na CBCN sukayi ga shugaban kasar

A kisan da ake ta fama dashi wanda Filani keyi a fadin kasar nan wanda ya hada da wasu malaman kirista guda biyu da akashe da kuma wasu mutane 15 a jihar Binuwai, manyan malaman kirista na Najeriya sunyi kira da shugaba Buhari akan ya sauka daga mulki.

CBCN sun bukaci shugaba Buhari ya daina wasu shawarwari game da yawan kisa da akeyi a fadin kasar, kawai ya sauka daga kan mulki kafin kasar ta ida rushewa baki daya, hakan zai kare masa mutuncinsa.

Malaman cocin Katolika na Najeriya sun bukaci shugaba Buhari ya sauka daga mulki
Malaman cocin Katolika na Najeriya sun bukaci shugaba Buhari ya sauka daga mulki

Shugaban malaman Rev. Augustine Akubeze da sakataren malaman Rev. Camillus Umoh, suka bayyana kiran wanda malaman na CBCN sukayi ga shugaban kasar, ta hanyar kafar yada labarai ta The Punch, a ranar Alhamis.

KU KARANTA KUMA: Mun rasa mutane 8 a harin da aka kawo jihar Binuwai - Sarkin hausawan Makurdi

A ranar Talata malaman suka bayyana cewa kisan da akayi na malaman cocin da wasu da sukaje bauta a cikin cocin a gabashin karamar hukumar Gwer, a jihar Binuwai, a matsayin rashin imani wanda dama can shiryashi akayi.

A halin da ake ciki, Buhari ya gargadi mutanen jihar Benuwe da kada su yarda wasu tsirarun mutane su dinga hada su fada saboda wata bukata tasu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=e

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng