Duniya Ta Zo Karshe: Annabin Karya Ya Sake Bayyana a Najeriya, Ya Ce Ya Ga Allah da Idonsa

Duniya Ta Zo Karshe: Annabin Karya Ya Sake Bayyana a Najeriya, Ya Ce Ya Ga Allah da Idonsa

  • Wani matashi a kasar Yarbawa ya zo da sabon salo, y afara kiran kansa Annabin Allah, kuma ya fi Annabi Musa Daraja
  • Wannan na zuwa ne bayan da a baya aka taba ganinsa dauke da wani gunkin Yarbawa, lamarin da ya jawo cece-kuce
  • An sha samun mutane da dama da ke karyar cewa su Annabawa ne, amma hujjoji da dama sun nuna akasin hakan

Jihar Oyo - Qudus Ewe, matashin malamin addinin Musulunci daga garin Saki, Jihar Oyo, wanda ya kai gunkin ‘Osanyin’ ga mawaki Portable a wasu makonni da suka gabata, yanzu ya bayyana kansa a matsayin Annabin Allah.

A cikin wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, Qudus Ewe ya bayyana cewa yana ganin Allah kuma yana magana da Shi kai tsaye.

Annabin karya ya bayyana a Najeriya
Yadda wani ke ikrarin zama Annabi | Hoto: Afa Qudus Ewe, Isaac Dachen, @yoruba_world
Asali: UGC

A yayin da wannan batu ya haifar da cece-kuce daga Musulmai da dama, iyalan Qudus sun fito fili sun karyata ikirarinsa tare da neman gafara daga jama’a.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda jirgin kasa ya bi ta kan mai barci, kuma ya rayu ya ba da mamaki

Jama’a sun fusata da aikin Alfa Qudus

Musulmai da dama sun bayyana bacin ransu game da wannan bidiyo da Qudus Ewe ya wallafa, inda ya yi ikirarin cewa ya fi Annabi Musa girma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin Al-Qur’ani mai girma, Annabi Musa yana daga cikin manyan manzanni kuma an ambace shi fiye da kowanne mutum a cikin Al-Qur'ani. Ana kyautata zaton Annabi Musa ya rayu a karni na 14 ko na 13 kafin zuwan annabta ta karshe.

Abin da yake ikrarin sani a kansa

A cikin bidiyon, Qudus ya ce:

"Na fi Annabi Musa girma. Na rantse da Allah. Ni Annabi ne. Annabin Allah ne. Annabi Musa ba ya mataki daya da ni."

Ya kara da cewa:

"Na ga Allah ido da ido. Wannan ba batun alfahari ba ne; kuma na san cewa ba kowa ba ne zai yarda da abin da nake fada.
"Na fi matsayin Alfa yanzu. Na fi matsayin Sheikh. Ni Annabin Allah ne. Allah ne da kansa ya kira ni Annabinsa.

Kara karanta wannan

'Muna cikin tashin hankali': Daruruwan mata sun fita zanga zanga a jihar Benuwai

"Annabi Musa ya ji muryar Allah ne kawai, amma bai gan shi ba. Amma ni ina ganinsa kuma ina jin muryarsa. Na rantse da Al-Qur’ani. Na rantse da ranar da zan kasance ni kadai a kabari. Na rantse da raina cewa ni Manzo ne, Annabin Allah."

Meye matsayin Muslunci game da Qudus?

Ikirarin Qudus ya sabawa koyarwar addinin Musulunci, kasancewar Musulmai sun yarda cewa babu wani Annabi da zai zo bayan Annabi Muhammad (SAW), wanda ake dauka a matsayin Annabi na karshe kuma Manzon Allah.

Mai ikrarin Annabta ya bayyana a Najeriya
Jama'ar Yarbawa a jihar Kudu maso Yamma | Hoto: @seyiamakinde
Asali: Twitter

A watan Janairu, an ga Qudus a yankin Iyana-Ilogbo na Jihar Ogun tare da gunkin ‘Oseyin’, wani tsohon gunkin adddinin gargajiyar Yarbawa, yana yi wa mawakin Portable addu’a.

Akwai rahotannin da ke cewa Qudus dan gargajiya ne kuma mafarauci, wanda ya gaji ‘Oseyin’ daga mahaifinsa, amma Legit bata iya tabbatar da hakan ba.

Annabin karshe a addinin Islama

A littafin addinin Islama, Al-Qur'ani, tuni an bayyana Annabi Muhammadu (SAW) a matsayin Annabin karshen zamani, wanda aka aiko ga ilahirin al'ummar duniya.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kutsa cikin gida a Kano, sun yi ta'asa bayan cirewa wani ƴan yatsu

Wannan na nufin, an rufe duk wata kofa ko kafa ga masu da'awar annabta a bayan Annabi Muhammadu.

Sai dai, an sha samun masu ikirarin annabta a lokuta da dama, daga ciki akwai wanda ya fito tun a lokacin da Annabi ke raye, inda ya bayyana karbar wahayi daga Allah kamar yadda Annabawa ke yi.

A nan Najeriya, an sha samun wasu da ke ikrarin hakan, amma da ke da'awa ce ta karya, babu wanda ya taba tasiri wajen samun karbuwar da ta yi bisa.

Haka nan, a kasashe da dama an sha samun masu ikirarin cewa su Annabawa ne, duk da sanin cewa ba zai yiwu a samu ba.

Yadda aka gano abin da ya aikata

Wani malamin addinin Musulunci daga Ilorin, Sanusi Lafiagi, ya wallafa bidiyon Qudus a shafinsa na Facebook, yana mai cewa:

"Wannan sokon shaidan ya rude shi. Ya ga daya daga cikin manyan wakilan Shaidan ya dauka cewa Allah ne. Ya kamata a nemo shi a tattauna da shi kafin ya jefa wasu cikin halaka da karya. Allah ya kare mu."

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Yaran Bello Turji sun sace ɗan Isiyaka Rabiu, matashin ya yi roko a bidiyo

Bayan wallafar Lafiagi, mutane da dama sun yi tsokaci, suna sukar Qudus Ewe, yayin da iyayensa suka fitar da bidiyo suna nesanta kansu da ikirarin da dansu ya yi.

An fadada labarin nan ta hanyar kara bayani kan samuwar Annabawan karya a lokuta daban-daban a tarihi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.