Annabin karya da ya fito daga kasar Amurka ya mutu, kwanaki kadan bayan ya kai ziyara kasar Kenya

Annabin karya da ya fito daga kasar Amurka ya mutu, kwanaki kadan bayan ya kai ziyara kasar Kenya

- Annabin karya da yake shiga irin ta Annabi Isa wanda ya fito daga yankin kasar Amurka ya mutu saboda ciwon sanyi

- Faston dai yayi suna a shafukan sada zumunta na duniya musamman ma a yankin Afirka, inda hotunansa suke ta yawo a lungu da sako na shafukan sada zumunta

- A satin da ya gabata ne kasar Kenya ta mayar dashi kasar ta Amurka, inda kuma shima faston da ya gayyato shi aka kama shi

Micheal Job, wani fasto ne dan kasar Amurka, wanda kwanan nan ya kai ziyara kasar Kenya a matsayin annabi, rahotanni sun nuna cewa Job ya mutu kwanaki kadan bayan ya kai ziyara kasar ta Kenya.

A cewar wani rahoto da wata jaridar kasar Kenya ta ruwaito, wata majiya daga asibitin Heyn Hospital ta tabbatar da cewa Michael Job ya kamu da ciwon sanyi inda yake karbar magani a asibitin.

KU KARANTA: Tirkashi: Sabuwar rigima ta barke tsakanin Adam A Zango da wata matar aure da ta zagi amaryarsa

Hotuna da bidiyo da aka dauke shi a lokacin da yayi shiga irin wacce Annabi Isa yake yi sun yada a shafukan sada zumunta irinsu Facebook, Twitter da kuma Instagram.

Makon da ya gabata ne dai aka mayar dashi kasarsa, inda kuma shima fasto din da ya gayyato shi aka kama shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng