Annabin 'yan Twitter: Wani ya yi da'awar shi Annabin Allah ne, ya shiga hannun hukuma

Annabin 'yan Twitter: Wani ya yi da'awar shi Annabin Allah ne, ya shiga hannun hukuma

  • An kama wani mutumin da ke da'awar cewa shi annabi ne, duk samunsa da aikata munanan abubuwa a duniya
  • Ya bayyana da'awarsa ne ta shafukan sada zumunta, inda yake cewa shi yana da karamomi, tare da bayyana dalilai
  • Sai dai, mutane da dama a shafin Twitter sun yi ta caccakarsa, inda suka ta yada tsofaffin hotunansa a gidan caca

Lebanon - An kama wani dan kasar Lebanon da ikrarin shi Annabi ne a birnin Beirut a ranar Litinin bayan da ya haifar da cece-kuce a shafukan sada zumunta, musamman tsakanin 'yan Twitter na Masar.

Nashat Munther ya wallafa wasu rubuce-rubuce a shafinsa mai taken "Annabi Nashat Majd Noor, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi" (wal iyazu billah), yana mai cewa shi Annabi ne da Allah ya aiko.

Kara karanta wannan

Nasara: 'Yan sanda sun halaka 'yan ta'adda 23, sun yi ram da 'yan bindiga 37 a Sokoto

Annabin Karya na Lebanon
Annabin 'yan Twitter: Wani ya yi da'awar shi Annabin Allah ne, ya shiga hannun hukuma | Hoto: @alosheofficial
Asali: Twitter

Ya buga shaidu da yawa da ya ce sun fito ne daga mabiyansa da suka yi ikirarin samun salama daga neman kusanci dashi.

A wani lokaci, ya hana jama'ar kasar Masar bin koyarwarsa, lamarin ya jawo cece-kuce sosai a shafin Twitter.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar An-Nahar ta kasar Lebanon ta ce jami'an tsaron sun kame Munther, tare da zarginsa da laifuka da dama, da suka hada da da'awar cewa shi Annabi ne, da yin barazana ga 'yan jarida, da kuma cin mutuncin wata kasa mai alaka da Lebanon, wato Masar.

A halin yanzu dai ana bincikensa kan wadannan zarge-zarge.

Bayan ya yi suna a yankin Gabas ta Tsakiya, tsofaffin hotunan da ke nuna shi yana buga ganguna a gidan caca ne masu amfani da kafofin watsa labarun suka yi ta yada wa don nuna rashin ingancinsa.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Likitan Bello Turji da ke masa jinya da kawo masa kwaya ya shiga hannu

Wani rubutu da @alosheoffical ya yada a Twitter a harshen larabci ya bayyana cewa:

"Jami'an tsaron kasar Labanon sun kama wanda ake kira "#Annabi_Nashat_Majd_Al-Nor" wanda kuma ya yarda cewa shi ba Annabi ba ne daga baya!!"

Kalli rubutun da larabci a kasa:

Annabin karya a Najeriya

A wasu shekaru a Najeriya, san samu wadanda suka yi ikrarin su ma annabawa ne.

A baya mun kawo rahoton cewa, daga cikin kasurguman kattin dai, Ayo Jimoh shine yake da'awar shi Annabi ne wanda hakan ya sa ta yadda da shi har ta bashi kudin ta makudai domin yayi mata addu'a.

Legit.ng Hausa ta samu cewa Jimoh din wanda ke da shekaru 45 a duniya, ya karbi Naira 266,000 a tashin farko sai kuma ya anshi sarkokin zinaren matar da suka kai Naira 750,000.

Da ya shiga hannun 'yan sanda, Mista Jimoh ya gasgata laifin da ake tuhumar sa da shi inda kuma ya bayyana cewa shi zinaren da ta bashi tuni ya saida su kuma suma kudaden ya kashe shu.

Kara karanta wannan

Kotu ta zabi ranar Valentine don yanke wa Hushpuppi hukunci a Amurka

Yanzu haka dai suna a gaban kotun majistare ta garin Ikorodu, jihar Legas inda 'yan sandan suka gurfanar da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel