Wani annabin karya ya bayyana a Najeriya

Wani annabin karya ya bayyana a Najeriya

Wasu kasurguman katta su biyu da daya daga cikin su ke ikirarin cewa shi Annabi ne masu suna Ayo Jimoh da Abdullahi Jubrila sun shiga hannun jami'an 'yan sandan Najeriya bayan sun damfari wata mata mai suna comfort Macaulay har Naira miliyan daya.

Daga cikin kasurguman kattin dai, Ayo Jimoh shine yake da'awar shi Annabi ne wanda hakan ya sa ta yadda da shi har ta bashi kudin ta makudai domin yayi mata addu'a.

Wani annabin karya ya bayyana a Najeriya
Wani annabin karya ya bayyana a Najeriya
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yan majalisar tarayya 62 za su fice daga APC

Legit.ng Hausa ta samu cewa Jimoh din wanda ke da shekaru 45 a duniya, ya karbi Naira 266,000 a tashin farko sai kuma ya anshi sarkokin zinaren matar da suka kai Naira 750,000.

Da ya shiga hannun 'yan sanda, Mista Jimoh ya gasgata laifin da ake tuhumar sa da shi inda kuma ya bayyana cewa shi zinaren da ta bashi tuni ya saida su kuma suma kudaden ya kashe shu.

Yanzu haka dai suna a gaban kotun majistare ta garin Ikorodu, jihar Legas inda 'yan sandan suka gurfanar da su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel