An damke wasu barayin shanu yayin da suke raba shanun da suka sata

An damke wasu barayin shanu yayin da suke raba shanun da suka sata

- Jami’an Sojin sunyi nasarar kama wasu mutane shida da ake zargin masu satar shanu ne a cikin daji a jihar Taraba

- An kamasu ne a Dajin Nyogor lokacin da suke cikin rabon shanun da suka sata daga wurin mutane

- Lt. Col. Sani Adamu kwamandan Sojin ya bayyana cewa a gano shanu 30 daga hannun wadanda ake zargin

A ranar Juma’a, 25 ga watan Maris, ne jami’an Sojin Najeriya dake jihar Taraba sukayi nasarar kama barayin shanu a cikin daji, lokacin da suke cikin rabon shanun da suka sata daga wurin mutane. Jami’an Soji na 20 Mechanised Battalion, Serti, da suke aiki a Mambilla, jihar Taraba ne suka kamasu a Dajin Nyogor.

An damke wasu barayin shanu yayin da suke raba shanun da suka sata
An damke wasu barayin shanu yayin da suke raba shanun da suka sata

DUBA WANNAN: Zamu fitar da sunayen barayin gwamnati da ke cikin APC - Jam'iyyar PDP

Shugaban kungiyar Sojin Lt Col. Sani Adamu, ya bayyana sunayen wadanda ake zargin: Hammanjulde Yahya, 50; Umaru Yahaya, 40; Paul Samuel, 35; Juli Adamu, 30; Ibrahim Yusufa, 27; da kuma Usumanu Buba, 25.

A lokacin da ake tasa keyarsu a Mayo-Ndaga a karamar hukumar Sardauna, Adamu ya bayyana cewa an samu shanu 30 daga hannun ‘yan ta’addan. Ya gargadi wadanda ke rike da dabbobin mutane na sata da su mayar dasu ga masu gari ko jami’an tsaro kafin a kamasu.

Wanda ke magana da ke magana da yawun hukumar Sojin, Mr. David Missal, ya bayyanawa jaridar Punch, a ranar Asabar cewa, duk da jami’an Sojin na mika wadanda suka kama ga hukumar ‘Yan Sanda, ba zai hana hukumar ta kara gudanar da bincike akansu ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164