Tsohon Soja Ya Ci Gyaran IBB, Ya 'Fallasa' Abin da Ya Shirya Wa Abacha a 1993
- Wani tsohon babban soja a mulkin Janar Ibrahim Babangida Babangida ya caccake shi bayan kaddamar da littafinsa a Abuja
- Janar Ishola Williams mai ritaya ya ce IBB ya shirya Abacha don karɓar mulki kafin soke zaɓen 12 ga Yuni 1993, ba tare da izininsa ba
- A cikin littafinsa, IBB ya amince da cewa MKO Abiola ya lashe zaɓen, amma ya ce Abacha ne ya soke nasararsa shi ba tare da izininsa ba
- Williams ya ce gwamnatin rikon kwarya da Ernest Shonekan ya jagoranta ba gaskiya ba ce, an shirya wa Abacha hanyar karbar ragama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Wani tsohon babban jami’in soji, Janar Ishola Williams (mai ritaya), ya ce IBB ya shirya Abacha don karɓar mulki kafin ya soke zaɓen 12 ga Yuni, 1993.
Williams, tsohon Babban Jami’in Horarwa da Tsare-Tsare na Sojojin Najeriya, ya ce abin da ke cikin littafin Janar Ibrahim Babangida akwai abubuwa da ba gaskiya ba.

Asali: Getty Images
Tsohon soja ya fadi shirin IBB ga Abacha
Williams ya bayyana hakan a shirin 'Inside Sources' na Channels TV a ranar Juma’a 28 ga watan Fabrairun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojan na cikin wadanda aka ambata a cikin littafin tarihin IBB mai shafuka 420 da aka kaddamar a Abuja a ranar 20 ga Fabrairu, 2025.
A shafi na 296, Janar Babangida ya ce wasu manyan sojoji kamar Salihu Ibrahim da Ishola Williams sun nuna ɓacin rai game da lamarin.
Kanal Dangiwa Umar mai ritaya ma ya yi barazanar murabus saboda an soke zaben.
Don fayyace abin da ya faru, Williams ya ce IBB ya riga ya shirya Abacha ya gaje shi tun kafin soke zaɓen 1993.
Ya kuma ce gwamnatin Ernest Shonekan ba gaskiya ba ce, domin kawai hanyar da aka tanada don bai wa Abacha damar karɓar mulki ce.

Kara karanta wannan
'Yadda Buhari ya dara Obasanjo, Yar'Adua da Goodluck Jonathan a lokacin mulkinsa'

Asali: Twitter
Wane suna IBB yake kiran Abacha?
Williams ya ce:
"IBB ya saba kiran Abacha ‘Khalipha’, yana nufin yana goyon bayansa don karɓar mulki, koda ya ke ba ya iya fadar hakan a fili."
A cewarsa, wata rana a Minna da misalin tsakar dare, ya tambayi IBB:
“Ko kun yi alkawari da Abacha cewa zai gaje ka?”
Amma ya ce IBB bai ba da amsa ba, a lokacin, wasu gwamnoni sun nemi IBB ka da ya mika mulki, amma Williams ya shawarce shi da ya sauka kawai.
A watan Agusta 1993, Williams ya aika wa IBB wasiƙa yana mai cewa mafi alheri shi ne sojoji su mika mulki ga farar hula.
IBB ya nada sababbin hafsoshin soji, amma Williams ya shaida musu cewa ba za su daɗe a ofis ba, wanda daga baya ya zama gaskiya.
A cewar Williams, dokar kafa gwamnatin rikon kwarya an tsara ta ne ta yadda Abacha zai samu damar karɓar mulki daga baya.

Kara karanta wannan
Littafin IBB: Fitaccen Lauya, Falana zai maka Janar Babangida a kotu, ya jero dalilai
IBB ya fadi dalilin tumbuke Buhari
A baya, kun ji cewa Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya fadi musabbabin kifar da Gwamnatin Janar Muhammadu Buhari a 1985.
IBB ya ce a lokacin mulkin Buhari, ya raba kan sojoji da kuma rashin jagoranci mai inganta na daga cikin dalilan rasa mulkinsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng