'Babu Hannu na': Gwamna Ya Wanke Kansa kan Zargin Mai Gidansa da EFCC Ke Yi na N700bn
- Gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno, ya nesanta gwamnatinsa daga zargin rashawa na ₦700bn da ake wa Udom Emmanuel
- Eno ya soki yadda ake ci gaba da fallasa tsofaffin gwamnonin jihar tun daga 1999, yana mai cewa hakan yana hana shugabanni yin aiki da kwazo
- Ya ce binciken rashawa kan shugabanni bayan sun bar mulki na iya hana sababbin shugabanni kokarin ba da gudunmawarsu gaba ɗaya ga al’umma
- Hukumar EFCC ta kama Emmanuel bisa zargin almundahanar ₦700bn, inda ake zarginsa da karɓar ₦3trn daga asusun tarayya, amma ya bar basukan ₦500bn
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Uyo, Akwa Ibom - Gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno, ya yi martani game da tuhumar tsohon gwamna, Udom Emmanuel da ke yi da cin hanci.
Gwamna Eno ya nesanta gwamnatinsa daga zargin rashawa na ₦700bn da ake yi wa Emmanuel inda ya ce bai san da haka ba.

Asali: Facebook
Musabbabin cafke tsohon gwamnan da EFCC ta yi
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin wani taro a Abak da ke jihar a ranar Asabar 8 ga watan Maris, 2025, cewar Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar Talata, 4 ga Maris, 2025, hukumar EFCC ta kama Udom Emmanuel bisa zargin rashawa na ₦700bn.
Ana zarginsa da karɓar ₦3trn daga asusun tarayya a shekara takwas, amma ya bar basukan ₦500bn da ayyukan da ba a biya ba na ₦300bn.
Wata ƙungiya ce ta shigar da ƙorafi kansa kan kuɗin da ya karɓa daga asusun tarayya da yawan basussukan da ya bari.
Gwamna ya kare kansa daga tuhumar mai gidansa
Eno ya ce kwata-kwata bai san da wannan lamari ba yayin da ke musanta fitowar wadannan kudade daga jihar.
Gwamna Eno ya ce:
“Ba mu san inda suka samo wadannan lambobi ba, domin ba su fito daga Akwa Ibom ba."

Asali: Twitter
Gwamna ya soki EFCC kan tuhumar tsofaffin gwamnoni
Gwamnan PDP din ya soki abin da ya kira ci gaba da fallasa tsofaffin gwamnonin jihar tun bayan dawowar dimokuradiyya a 1999.
Ya kara da cewa:
“Yadda muke mu’amala da shugabanninmu bayan sun yi aiki tukuru yana da matukar damuwa."
Ya kuma ce binciken rashawa kan shugabanni bayan sun bar mulki yana hana sababbin shugabanni yin aiki da kwazo, cewar rahoton Vanguard.
“Na riga na shirya cewa hakan zai faru da ni, amma yana hana shugabanni kokari saboda ba sa samun godiya da yabo."
- Cewar Gwamna Eno
Gwamna ya sha alwashi bayan kammala mulki
Kun ji cewa Gwamnan jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno ya yi magana kan abubuwan da ke faruwa a siyasar jiharsa a ƴan kwanakin nan.
Yayin da yake martani ga wata ƙungiya da ta nemi a turo masa EFCC da ICPC, Gwamna Eno ya ce a shirye yake ya tuɓe rigar kariya kuma ya miƙa kansa.
Fasto Eno ya ce duk masu burin haɗa shi faɗa Bola Tinubu, Godswill Akpabio ko ubangidansa, Udom Emmanuel ba masoyan jihar Akwa Ibom ba ne.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng