'Abubuwan da Ya Kamata Musulmi Su Dage da Yi a Watan Azumin Ramadan'
- Gwamna Umaru Bago ya bukaci al'ummar musulmi su dage da addu'o'i domin samun zaman lafiya da ci gaba a Neja da kasa baki ɗaya
- Muhammed Bago ya ce watan Ramadan wata ne mai albarka wanda ke cike da gafara, rahama da ƴantawa ga masu azumi domin Allah
- Ya kuma jaddada shirin gwamnatinsa na rabon kayan abinci ga masu karamin karfi, inda ya roki waɗanda aka naɗa su yi adalci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Niger - Gwamnan jihar Neja, Muhammad Umaru Bago, ya ba al'ummar musulmi shawara kan abubuwan da ya kamata su maida hankali a kai domin ribatar watan Ramadan.
Ya ce wannan wata mai alfarma na Ramadan yana da muhimmanci sosai ga musulmi, don haka ya kamata a yi amfani da shi wajen sabunta dangantaka da Allah tare da neman shiriya da albarka.

Asali: Facebook
Abubuwan ya kamata musulmi su yi a Ramadan
Gwamna Bago ya bukaci musulmin Neja da su dage da yin addu’o’i domin samun zaman lafiya, ci gaban kasa, da kuma ci gaban jihar, kamar yadda Tribune Nigeria ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bago ya bayyana hakan ne a sakon taya murna da fatan alheri ga musulmi bisa shigowar watan Ramadan wanda kakakin gwamnan, Bologi Ibrahim ya fitar.
Gwamna Bago ya ƙara da cewa Ramadan wata ne na ibada da rahama, wanda ke kawo albarka, dacewa da gafara ga masu yin azumi da iklasi watau don Allah.
Ya bukaci musulmin Neja da su yi amfani da wannan lokaci na ibada wajen yin addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya a jihar, da kuma fatan samun shugabanci nagari a Najeriya baki daya.
Gwamna Bago zai raba tallafin kayan abinci
Gwamnan ya kuma jaddada muhimmancin nuna tausayi da kyautatawa ga marasa galihu, inda ya sanar da rabon kayan abinci domin tallafawa mabukata a lokacin azumi.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun ɓullo da sabuwar dabara, mataimakin ciyaman ya faɗa tarko a Zamfara
Ya ce gwamnatinsa ta samar da kayan abinci da za a raba ga mabukata domin saukaka musu wahalar da ka iya biyo bayan tsadar kayayyakin masarufi da azumi.
Gwamna Bago ya bukaci wadanda aka dorawa alhakin raba kayan tallafin da su yi adalci da gaskiya, su tabbatar da cewa kayan sun isa ga wadanda aka nufa da su ba tare da nuna son kai ko fifiko ba.
Dalilin rabawa talakawa abinci a Ramadan
Gwamnan ya ce manufar rabon kayan abincin ita ce rage radadin tattalin arziki da ke addabar marasa karfi a jihar Neja.
A karshe, Gwamna Umaru Bago ya taya daukacin musulmi murna da zuwan watan Ramadan.

Asali: Twitter
Ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da yin aiki tukuru domin inganta rayuwa da jin daɗin al’ummar jihar Neja.
Ya kuma yi fatan Allah Ya sa ayi azumi lafiya kuma karɓaɓɓe tare da samun nasarori da albarkar wannan wata mai tsarki.
Farashin abinci ya karye a kasuwanni
A wani rahoton, kun ji cewa farashin kayan abinci da aka fi amfani da su a yau da kullum sun sauka a kasuwannin Arewa.
Wani bincike da aka yi ya nuna cewa an samu saukin farashin masara, shinkafa, gero, dawa da wake musamman a jihohin da ake samar da su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng