'Dan Majalisar Amurka Ya Fadi Hukumar da Ke Taimakawa Boko Haram da Ta'addanci

'Dan Majalisar Amurka Ya Fadi Hukumar da Ke Taimakawa Boko Haram da Ta'addanci

  • Dan majalisar Amurka, Scott Perry, ya zargi hukumar USAID da taimaka wa kungiyoyin ta'adda, ciki har da Boko Haram
  • Perry ya ce ana kashe $697m a kowace shekara, kuma babu hujjar gina makarantu 120 da aka ce an yi a kasar Pakistan
  • Ya kara da cewa kudin da ake ikirarin ana taimaka wa mata, ba su kai gare su ba, sai ma taimaka wa harkar ta'addanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Washington DC, America - Dan majalisar Amurka, Scott Perry, ya bayyana cewa hukumar bayar da tallafin Amurka, USAID, ta bai wa kungiyoyin ta'addanci kudi, ciki har da Boko Haram.

'Dan Majalisar ya ce ana kashe makudan kudi na miliyoyin daloli kowace shekara domin kungiyoyin ISIS, Al-Qaeda da Boko Haram.

Dan Ya zargi Hukumar USAID da saukar nauyin ta'addanci
Dan Majalisa a Amurka, Scott Perry ya zargi USAID da taimakawa Boko Haram da sauran yan ta'adda. Hoto: The Hill, HQ Nigerian Army.
Asali: Facebook

'Dan Majalisa ya zargi USAID da ta'addanci

Kara karanta wannan

'Suna jawo bala'i': Basarake ya haramta ayyukan bokaye mata bayan kisan dan majalisa

Perry da ke wakiltar Pennsylvania, ya yi wannan ikirari a taron farko na kwamitin kula da ingancin ayyukan gwamnati, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

“Kudin tallafin dala miliyan 697 a kowace shekara, da sauran kudaden da ake tura wa ISIS, Al-Qaeda, Boko Haram suna taimaka wa ta'addanci.”

Kwamitin ya ce zai hada hannu da ma'aikatar ingancin gwamnatin shugaba Trump domin bincike kan yadda ake almubazzaranci da kudaden haraji.

Perry ya kuma zargi USAID da kashe $136m don gina makarantu 120 a Pakistan, amma babu wata shaida da ke nuna an gina su, The Sun ta ruwaito.

Ya ce:

“Ana zargin cewa kudin da ake cewa ana taimaka wa mata a Afghanistan, a zahiri ba su kai gare su ba, ana taimaka wa ta'addanci ne.”
"USAID ta kashe $840m a shekaru 20 da suka gabata kan ilimin Pakistan, amma babu wata shaida da ke tabbatar da hakan.”

Trump yana zargin USAID da cin hanci

Kara karanta wannan

Jarumar Kannywood ta koma kotu kan neman saki daga mijinta, alkali ya ba da umarni

Shugaba Donald Trump ya taba kiran a rufe hukumar USAID saboda zargin cin hanci da ake yi wa hukumar.

Elon Musk, wanda Trump ya nada shugaban ma'aikatar ingancin gwamnati, ya ce USAID tana gudanar da ayyukan sirri na CIA.

Musk ya ce hukumar na yi wa Amurka zagon kasa, kuma zai tabbatar da an rufe ta domin rage yawan kashe kudaden gwamnati.

Yadda dan ta'adda ya yi mutuwar wulakanci

Mun ba ku labarin cewa wani babban 'dan bindiga da ake kira Kachalla Dan Lukuti, ya rasu bayan fama da wata muguwar cuta.

An tabbatar da cewa kafin mutuwarsa sai da ya fara haushin kare wanda ya tilasta sauran yan uwansa kaurace masa gaba ɗaya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.