Jarumar Kannywood Ta Koma Kotu kan Neman Saki daga Mijinta, Alkali Ya ba da Umarni

Jarumar Kannywood Ta Koma Kotu kan Neman Saki daga Mijinta, Alkali Ya ba da Umarni

  • Jarumar Kannywood, Maryam Malika, ta roki kotun Shari’a da ke Magajin Gari, Kaduna, ta tabbatar da sakin da tsohon mijinta, Umar, ya yi
  • Lauyanta ya bayyana cewa tsohon mijin nata ya yi mata furucin saki na uku shekaru biyar da suka wuce bayan ta nemi saki ta hanyar Khul’i
  • Alkalin kotun ya umarci a ci gaba da kokarin isar da sammaci ga wanda ake kara ta wata hanya sannan ya dage shari’ar zuwa 27 ga Fabrairu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Kaduna - Jaruma a masana'antar Kannywood, Maryam Muhammad, da aka fi sani da Maryam Malika ta sake shigar da mijinta kara a kotu.

Jarumar Kannywood, Malika ta roki kotun Shari’a da ke Magajin Gari, Kaduna, da ta tabbatar da sakin da tsohon mijinta, Umar, ya yi tun a shekarun baya.

Kara karanta wannan

Arewa: El-Rufa'i ya aika gargadi ga APC da Tinubu kan zaben 2027

Jarumar Kannywood ta kai karan mijinta kotu kan saki
Jaruma Maryam Malika ta roki kotu ta tabbatar da sakin da mijinta ya yi mata. Hoto: Kannywood Celebrities.
Asali: Facebook

Yadda mijin Malika ya sake ta a baya

Lauyan Maryam, A.S Ibrahim, ya shaida wa kotun cewa wanda ake kara ya yi furucin saki na uku shekaru biyar da suka wuce bayan ta nemi saki ta, cewar Daily Nigerian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ya yi furucin saki sau biyu bayan ta kai kara kotu tana neman saki ta hanyar Khul’i."
"An kai masa sammaci daga kotu sai ya rubuta furucin saki na uku a jikin takardar isarwar, wanda ta karanta ta ci gaba da rayuwarta ba tare da komawa kotu ba."

- In ji lauyan

An nemi wanda ake kara a kotu an rasa

Sai dai wanda ake kara bai halarci zaman kotun ba da aka yi a yau Laraba 12 ga watan Janairun 2025 kuma bai turo wakili ba.

Alkalin kotun, Kabir Muhammad, ya tambayi mai isar da sakon kotu ko ya kai sammaci ga wanda ake kara? ya kuma bayyana cewa bai same shi a gida ba.

Kara karanta wannan

CBN ya kawo sabon tsarin cire wa 'yan Najeriya kudi wajen aiki da ATM

Alkalin ya umarci a ci gaba da kokarin isar da sammaci ta wata hanya sannan ya dage shari’ar zuwa ranar 27 ga Fabrairun 2025 da muke ciki.

Malika ta fadi halin da 'yan fim ke ciki

A baya, mun ba ku labarin cewa jarumar masana’antar Kannywood, Maryam Malika ta yi martani a kan yadda mutane ke yi wa jarumai mata shaidar kin zaman aure

Malika ta bayyana cewa ranta ya kan baci idan ta ga yadda mutane ke mantawa da kaddara wajen shafa masu wannan bakin fenti musamman game da zaman aure.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.