Najeriya Ta Amince da Karin Kudin Kira da 50%, 'Yan Kasa Za Su Kashe N6.74tn a Waya
- Hukumar NCC ta amince da karin farashin kira zuwa N16.5 a kowace minti, wanda zai kara kudaden shiga na kamfanonin sadarwa
- Bincike ya nuna cewa jimillar kiran gida da aka yi a shekarar 2023 sun kai mintuna biliyan 408.5, inda MTN ta jagoranci a samun kira
- A sabon farashin, ana hasashen MTN za ta samu kudaden shiga da suka haura Naira tiriliyan 4 daga kiran da aka yi da aka karɓa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta amince da karin 50% na farashin wanda ke nufin matsakaicin farashin kira ya kai Naira 16.5 a kowane minti.
Wasu ‘yan Najeriya da su ka zanta da Legit sun koka a kan yadda ake fama da matsalar sabis din waya, sannan kuma aka samar da sabon karin farashi.

Asali: Twitter
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, bisa ga bayanan da hukumar NCC ta fitar a kan amfani da waya a 2023, wannan karin na iya samar wa kamfanonin sadarwa sama da N6.74tn a shekarar 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai wannan hasashen bai hada da tasirin rangwame da kiran kyautan kiran waya ba, wadanda ka iya rage yawan kudaden shiga da za a samu.
Yadda ‘yan kasa ke kashe kudin waya
Bayanai daga rahoton 2023 Subscriber/Network Performance na NCC ya nuna cewa a shekarar 2023, jimillar lokutan kiran da aka yi daga wayoyi sun kai mintuna biliyan 205.3,
Rahoton ya kara da cewa yayin da lokutan kiran da aka karɓa suka kai mintuna biliyan 203.2.
Rahoton ya ce:
"A watan Disamba 2023, jimillar kiran da aka yi daga cikin gida da na kasa sun kai mintuna 205,298,114,995.11, yayin da jimillar kiran da aka karɓa suka kai mintuna 203,187,588,876.00. MTN ta fi yawan samun kira inda ta yi mintuna biliyan 122.7 daga kira da kuma mintuna biliyan 123.8 na kira da aka karɓa a shekarar 2023."
Wannan yana nuna cewa ‘yan Najeriya sun shafe kimanin mintuna biliyan 408.5 suna yin kiran gida a shekarar 2023.
NCC ba ta sake sabon rahoto ba
Saboda rashin sababbin bayanai na 2024, bincikenmu NCC ya dogara ne da bayanan 2023, wanda ka iya bambanta da shekarar 2025.
Haka kuma, binciken bai hada da kiran kasa da kasa ba, duk da cewa ‘yan Najeriya sun shafe mintuna biliyan 1.5 suna yin kiran kasa da kasa a 2023.
Bincike ya kara nuna cewa MTN ta jagoranci kasuwar, inda ta samu mintuna biliyan 122.7 na kiran da aka yi da kuma mintuna biliyan 123.8 na kiran da aka karɓa.
A sabuwar farashin Naira 16.5 a kowane minti, ana hasashen cewa kudaden shiga na MTN daga kiran da aka yi da aka karɓa za su haura Naira tiriliyan 4.
NCC ta amince da karin kudin waya
A baya, mun ruwaito cewa Kamfanonin sadarwa sun samu yadda su ke so bayan gwamnatin tarayya ta hannun hukumar sadarwa ta ƙasa watau NCC ta amince da karin kudin kira.
Mai magana da yawun NCC, Reuben Mouka ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin 20 Janairu, 2025, kuma ya sanar da cewa a amince da su yi karin da 50%.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng