"Tinubu Zai Sha Wahala": LP Ta Bayyana Wanda Za Ta Tsayar Takarar Shugaban Ƙasa a 2027
- Jam'iyyar LP ta bayyana shirinta na sake bai wa tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi tikitin takarar shugaban ƙasa a zabe mai zuwa
- Mai magana da yawun LP na ƙasa, Abayomi Arabambi ne ya faɗi hakan a wata hira da aka yi da shi ranar Laraba, 12 ga watan Fabrairu
- Ya kuma maida martani ga Kenneth Okonkwo, wanda ya fice daga LP kwanan nan, yana mai cewa tafiyarsa alheri ce ga jam'iyyar tasu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - A yayin da ake shirin tunkarar zaben 2027, LP ta bayyana cewa za ta sake tsayar da tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, a matsayin dan takarar shugaban ƙasa.
Idan ba ku manta ba Mista Obi ya tsaya takarar shugaban kasa a karkashin LP a 2023, amma ya sha kaye a hannun Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC.

Asali: Facebook
Da yake jawabi a cikin shirin siyasa a yau na tashar Channeƙs TV, mai magana da yawun jam'iyyar LP na ƙasa, Abayomi Arabambi ya ce za su ba Obi dama a karo na biyu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta tattaro cewa tsohon gwamnan ya ba mutane da dama mamaki da ya zo na uku a yawan ƙuri'u a zaben 2023, yayin da da Atiku Abubakar na PDP ya zo na biyu.
2027: Bola Tinubu zai fuskanci kalubale inji LP
A hirar da aka yi da shi kan wanda za su tsayar takara, kakakin LP ya ce Shugaba Bola Tinubu ba zai lashe zaben 2027 cikin sauƙi ba, zai fuskancin babban ƙalubale.
“Tinubu ba zai samu nasara cikin sauki a 2027 ba, domin za mu dawo da Peter Obi a karo na biyu, don su gane cewa mun kuduri aniyar yin nasara,” in ji shi.
Arabambi ya soki Kenneth Okonkwo, tsohon mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Obi a 2023, wanda ya fice daga jam’iyyar LP kwanan nan.

Kara karanta wannan
An fara juyawa Tinubu, Atiku da Peter Obi baya game da zaben shugaban ƙasa na 2027
Jam'iyyar LP ta caccaki Kenneth Okonkwo
Ya bayyana ficewar Okonkwo daga LP a matsayin abu mai kyau da alheri ga jam’iyyar, yana mai zargin cewa tsohon dan wasan kwaikwayon yana yi wa Tinubu da jam’iyyar APC aiki.
Duk da haka mai magana da yawun LP ya ce suna yi wa tsohon jigon fatan alheri, amma ficewarsa daga jam'iyyar ya masu daɗi.
“Muna yi wa Kenneth Okonkwo fatan alheri, barinsa jam'iyyar LP kamar waraka ce daga wata cuta. Ya kamata ya daina magana kan jam’iyyarmu,” in ji Arabambi.
Ya kuma musanta cewa jam’iyyar LP tana fuskantar rikici ko barazana na rugujewa, yana mai cewa dukkan maganganun da ake yi kan hakan ba gaskiya ba ne, rahotoɓ Daily Post.
Okonkwo ya ba Tinubu, Atiku a Obi shawara
Kun ji cewa jarumin Nollywood kuma tsohon jigon LP, Kenneth Okonkwo ya ce lokaci ya yi da Bola Tinubu, Peter Obi da Atiku Abubakar za su matsa gefe a siyasar ƙasar nan.
Okonkwo ya bayyana cewa bai kamata manyan ƴan siyasar uku su sake fitowa takara ba a zaɓen na gaba, yana mai cewa hakan zai ba wasu damar nuna bajintarsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng