Duk da Yin Sulhu, 'Yan Bindiga Sun Tafka Ta'asa a Jihar Kaduna

Duk da Yin Sulhu, 'Yan Bindiga Sun Tafka Ta'asa a Jihar Kaduna

  • Wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hare-haren ta'addanci a jihar Kaduna da ke yankin Arewa
  • Ƴan bindigan waɗanɗa suka sanya kayan sojoji sun farmaki ƙauyukan ne na ƙaramar hukumar Kagarko da tsakar rana
  • A yayin farmakin da suka kai sun yi awon gaba da mutane 16 tare da ƙona gidaje da kayan amfanin gona masu yawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Kaduna.

Ƴan bindigan sun sace mutum 16 tare da ƙona wasu gidaje a ƙauyukan Makeri, Mai-Ido da Kushumi da ke ƙaramar hukumar Kagarko a jihar Kaduna.

'Yan bindiga sun kai hari a Kaduna
'Yan bindiga sun sace mutane a Kaduna Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce wani jagoran al’umma daga yankin, ya tabbatar da aukuwar lamarin ta wayar tarho a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka yi ta'asa a Kaduna

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun dakile harin 'yan bindiga bayan sun gwabza fada a Katsina

Ya bayyana cewa ƴan bindigan sun kai hare-haren a ne a ranar Litinin da misalin ƙarfe 12:00 na rana.

Shugaban al'umman ya bayyana cewa ƴan bindigan sun zo da yawa, inda wasu daga cikinsu suke sanye da kayan sojoji tare da riƙe mugayen makamai irinsu AK-47.

Ya ce ƴan bindigan sun kai hari ƙauyukan guda uku ne tsakar rana a lokacin mutane da dama sun tafi gonakinsu.

Ya ƙara da cewa mutanen da aka sace sun haɗa da mata 11 da yara biyar, inda aka yi awon gaba da su bayan an yi harbe-harbe.

"Ƴan bindigan sun yi amfani da lokacin da maza suka tafi gona. Sun farmaki ƙauyuka uku tare da ƙona wasu gidaje da amfanin gona."

- Wani shugaban al'umma

Ya bayyana cewa an sanar da dakarun sojoji da ke garin Kagarko, amma kafin su iso, ƴan bindigan sun tsere da mutanen da suka sace.

"Amma da safiyar yau an sanar da ni cewa dakarun sojoji suna bin sawun ƴan bindiga a yankin Hayin-Dam da dajin Kurutu, wanda ke kan iyaka da ƙaramar hukumar Kachia."

Kara karanta wannan

Janar Tsiga: Yadda 'yan bindiga suka shammaci jama'a, suka sace tsohon shugaban NYSC

- Wani shugaban al'umma

Jagoran al’ummar ya ce wasu daga cikin mazauna ƙauyukan sun tsere zuwa garin Kagarko da ƙauyen Janjala domin neman mafaka.

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Jami'an sandan yankin sun tabbatar da aukuwar lamarin amma ba su yi ƙarin bayani ba.

Hakazalika ba a samun jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Hassan Mansur, ba.

An yi zanga-zanga kan ƴan bindiga a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa hare-haren ƴan bindiga sun tilastawa mutanen ƙaramar hukumar Kachia fitowa kan tituna domin nuna adawarsu.

Mazauna Unguwan Ate sun gudanar da zanga-zangar ne domin ankarar da mahukunta halin da suke ciki na samun yawaitar hare-haren ƴan bindiga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng