Yadda Farfesa Yusuf Ya Ragargaji Tinubu kan Alaka da Faransa kafin a Kama Shi

Yadda Farfesa Yusuf Ya Ragargaji Tinubu kan Alaka da Faransa kafin a Kama Shi

  • Farfesa Usman Yusuf ya bayyana cewa tun bayan fara sukar gwamnatin Bola Tinubu, jami’an tsaro suke bibiyarsa
  • Tsohon shugaban hukumar NHIS ya ce jawabinsa a taron matasan Arewa a Bauchi ne ya jawo masa matsala da EFCC
  • A jawabinsa, ya lissafo abubuwa 10 da ke ci wa Arewa tuwo a kwarya, yana mai bukatar matasa su farka su ceto yankin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban hukumar inshora ta NHIS, Farfesa Usman Yusuf, ya bayyana cewa tun bayan fara sukar manufofin gwamnatin Tinubu jami’an tsaro ke bibiyarsa.

A cikin wata wasika da ya fitar daga gidan yari, Farfesa Yusuf ya ce hukumomin tsaro sun kama shi ne sakamakon jawabinsa a taron matasan Arewa da aka gudanar a Bauchi.

Kara karanta wannan

'Suna murna kamar sun cafke Bello Turji,' Farfesa Yusuf kan yadda aka kama shi

Usman Yusuf
Maganganu 10 da Farfesa Yusuf ya yi a taron matasan Arewa kafin a kama shi. Hoto: Muhammad Kime
Asali: Facebook

Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya wallafa a Facebook cewa Farfesa Yusuf ya yi jawabi mai zafi a taron, inda ya bayyana matsalolin da ke addabar yankin Arewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jawabin Farfesa Yusuf a taron Bauchi

Farfesa Usman Yusuf, ya bayyana abubuwa 10 da ke nuna gazawar gwamnati da kuma matsalolin da ke ci wa Arewa tuwo a kwarya:

1. Maganar zaben Tinubu a 2023

Farfesa Yusuf ya ce duk da cewa Arewa ta ba Bola Tinubu kashi 62% na kuri’un zaben, ita ce ke shan wahalar da gwamnati ke haddasawa.

Ana zargin gwamnatin Bola Tinubu da yin abubuwan da suka fusata mutanen yankin Arewa, watakila hakan zai iya taba APC a zaben 2027.

2. Matsalar tikitin Muslim-Musulim

Bola Tinubu ya dawo da abin da ba a taba gani ba a babbar jam'iyya tun 1993 lokacin da MKO Abiola ya jawo Babagana Kingibe suka yi takara.

Kara karanta wannan

Yadda gwamnatin tarayya ta nemi ba ni rashawar N5bn," Ɗan takarar shugaban ƙasa

Tsohon shugaban NHIS ya bayyana cewa tikitin Muslim Muslim da APC ta yi a 2023 wata dabarar siyasa ce da ta raba kan ‘yan Arewa.

3. Shirya rarraba Arewa

Ya bayyana cewa akwai wata makarkashiya da ke haddasa rashin tsaro da rikice-rikicen kabilanci da addini a Arewacin Najeriya.

4. Tabarbarewar tsaro

A yayin taron, ya bayyana cewa matsalar Boko Haram, ‘yan bindiga da rikice-rikicen kabilanci sun dagula zamantakewar Arewa.

A Yulin 2023 ne shugaban kasa ya nada sababbin hafsun tsaro, kuma bayan nan an ji yana cewa gwamnatinsa ta yi kokari a fannin.

5. Durkushewar sarautar gargajiya

Farfesa Usman Yusuf ya yi magana kan yadda ake ci gaba da lalata martabar sarautun gargajiya a jihohin Kano da Adamawa.

Sai dai gwamnatocin jihohi ne ke da iko a kan harkar masarautu, duk da ana zargin tarayya da katsalandan a kan sha'anin jihar Kano.

Kara karanta wannan

2027: Ganduje ya sha rubdugu da ya fara tallata Tinubu ga 'yan Arewa

6. Amfani da malamai

Ya zargi gwamnati da amfani da wasu malamai domin kwantar da hankalin al’umma yayin da ake kara jefa su a wahala.

7. Aiki da mawakan siyasa

Haka zalika ya ce gwamnati na daukar mawakan Hausa domin rura wutar gaba tsakanin ‘yan Arewa da mutanen kasar Nijar.

Kwanan nan aka ji cewa Dauda Kahutu Adamu da aka fi sani da Rarara ya yi waka, ya na caccakar shugaban jamhuriyyar Nijar.

8. Rashin kyakkyawar alaka da Nijar

Farfesa Yusuf ya yi gargadin cewa ficewar Mali, Burkina Faso da Nijar daga ECOWAS babban barazana ne ga Arewa.

9. Dangantaka da Faransa

Yayin taron matasa a jihar Bauchi, Farfesa Yusuf ya ce Tinubu na hulda da Faransa ta yadda hakan zai shafi tsaron Najeriya da Afirka ta Yamma.

A watan nan ne fadar shugaban kasa ta sanar da cewa Mai girma Bola Tinubu zai tafi Faris.

Kara karanta wannan

Arewa: El-Rufa'i ya aika gargadi ga APC da Tinubu kan zaben 2027

10. Matsalar tattalin arziki

A karshe, ya bukaci gwamnati da ta sake duba manufofinta na tattalin arziki da ke jefa talakawa cikin wahala.

Kiran Farfesa Yusuf ga matasan Arewa

A karshe, Yusuf ya bukaci matasan Arewa da su kasance tsintsiya madaurinki daya, su guji tashin hankali, kuma su shiga harkar siyasa ba tare da son zuciya ba.

Ya kuma yi gargadin cewa ka da matasa su bari a yaudare su da addini ko kabilanci domin a raba su.

ACF ta yi raddi ga Ganduje kan 2027

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar Arewa ta ACF ta yi martani ga shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje kan zaben 2027.

ACF ta ce Ganduje ba shi da hurumin cewa sai Bola Tinubu ya yi wa'adi biyu a kan mulki kafin wasu 'yan siyasar Arewa su tsaya takara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng