Halin Wasu Gwamnoni Ya Kara Fitowa, NLC Ta Koka kan Zaman da Suke Yi a Abuja

Halin Wasu Gwamnoni Ya Kara Fitowa, NLC Ta Koka kan Zaman da Suke Yi a Abuja

  • Ƙungiyar kwadago ta ƙasa watau NLC ta koka kan yadda gwamnoni da dama suka koma zama a birnin tarayya Abuja maimakon jihohinsu
  • Shugaban NLC, Kwamared Joe Ajaero ya ce rashin zaman gwamnonin a jihohin da suke mulki yana jawo koma baya a harkokin gwamnati
  • Ajaero ya bayyana cewa NLC ta ziyarci jihohi akalla biyar amma a jiha ɗaya ta tarar da mai girma gwamna, sauran kuma duk suna can Abuja

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kogi - Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta zargi gwamnoni da sakaci da harkokin mulki a jihohinsu, tana mai cewa sun fi zama a babban birnin tarayya, Abuja.

NLC ta koka cewa a daidai loƙacin da ƴan ƙasa ke fama da matsin rayuwa, galibin gwamnoni sun gudu, sun koma rayuwa a birnin Abuja maimakon zama a jihohinsu.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi fallasa, ya bankado masu siyarwa matasa takardun daukar aiki

NLC da gwamnoni.
NLC ta koka kan yadda gwamnoni ke yawan tafiya Abuja su bar jihohinsu Hoto: @NLCHeadquaters
Asali: Twitter

Shugaban NLC, Kwamared Joe Ajaero, ne ya faɗi hakan a taron tattaunawa da ma’aikata wanda ya gudana a hedikwatar NLC da ke Lokoja, jihar Kogi, Tribune ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NLC ta gano halin wasu gwamnonin jihohi

Ajaero ya nuna takaici kan yadda gwamnoni ke yawan zama a Abuja, yana mai cewa daga cikin jihohi biyar da kungiyar ta kai ziyara, a daya tak ne suka samu damar haduwa da gwamna.

"Yawancin gwamnoni yanzu sun koma zama a Abuja. Mun ziyarci kusan jihohi biyar, amma sai a daya ne muka hadu da gwamna. Duk lokacin da muka zo, sai a ce suna Abuja, hakan na taɓa mulki,"

- in ji Ajaero

Taron da aka shirya domin bai wa ma’aikata damar bayyana korafinsu, ya zo ne daidai lokacin da NLC ta kaddamar da motocin bas guda 10 masu amfani da iskar gas (CNG) domin rage wa ma’aikata radadi.

Kara karanta wannan

'Ka taka masa birki': An kai karar El Rufai gaban Nuhu Ribadu, an hango hatsarin kalamansa

NLC: "Ma'aikata na wahala a ƙasar nan"

Ajaero ya ce duk wata wahala da ta taso a kan ma'aikata take ƙarewa, yana mai misalta hauhawar farashin kayayyaki da shirin gwamnati na kara kuɗin sadarwa.

Ya jaddada cewa dole ne gwamnoni su zauna a jihohinsu don tabbatar da cewa dimokuradiyya na amfanar da al’umma, rahoton Vanguard.

"Wannan kamar dawowa gida ne a gare mu. Muna so mu tattauna da su domin mu ga ko suna yin abubuwan da a da muke sukar wasu a kansu," in ji Ajaero.

NLC za ta kai ƙorafe-korafe ga gwamna

Ma’aikatan Kogi sun yi amfani da damar taron sun faɗi matsalolinsu, da suka hada da rashin karin albashi duk shekara, rashin gidaje ga ma’aikata, da kuma karancin malamai a makarantu.

Kwamared Ajaero ya tabbatar da cewa NLC za ta kai koke-koken da suka zayyana mata kai tsaye ga gwamnan, muddin yana nan a jihar.

Kara karanta wannan

Rusau: Abba zai kashe biliyoyi wajen yin asibiti, tituna, lantarki a Rimin Zakara

"Duk ƙorafin da kuka mana za mu mika wa mai girma gwamna idan yana nan, idan kuma baya nan za mu bai wa wakilinshi," in ji shugaban NLC.

Kungiyar NLC ta janye zanga-zanga

A wani labarin, kun ji cewa ƴan kwadago sun dakatar da zanga zangar da aka shirya yi domin nuna adawa da ƙarin kudin kira a Najeriya.

Hakan ya biyo bayan matakan da gwamnatin tarayya ta ɗauka a taron da ta shirya da kungiyar NLC a Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262