Gwamna Ya Yi Fallasa, Ya Bankado Masu Siyarwa Matasa Takardun Daukar Aiki

Gwamna Ya Yi Fallasa, Ya Bankado Masu Siyarwa Matasa Takardun Daukar Aiki

  • Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya koka kan rashin gaskiyar da wasu jami'an gwamnati suka yi wajen ɗaukar malaman makaranta aiki
  • Abdullahi Sule ya bayyana cewa jami'an gwamnatin sun karɓi kuɗi a hannun matasa domin siyar musu da takardun ɗaukar aiki
  • Gwamna ya nuna cewa za a haɗa jami'an gwamnatin da hukumomin tsaro domin su girbi abin da suka shuka na rashin gaskiya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana wata badaƙala da jami'an gwamnati suka yi a jihar.

Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana yadda jami’an gwamnati suka sayar da takardun aiki 2,277 ga masu neman aikin koyarwa a jihar Nasarawa.

Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa
Gwamna Abdullahi Sule ya koka kan nuna rashin gaskiya a wajen daukar aiki Hoto: Abdullahi A. Sule
Asali: Facebook

Jami'an gwamnati sun yi rashin gaskiya a Nasarawa

Gwamnan ya yi barazanar mika jami’an da aka dakatar daga hukumar kula da syyukan malamai ta jihar Nasarawa (NSTSC) ga hukumomin tsaro saboda karɓar kuɗi daga masu neman aikin koyarwa, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Abinci ya ƙare: Gwamna ya tattara duka masu muƙaman siyasa, ya kore su daga aiki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Sule ya yi wannan furuci ne bayan karɓar rahoton kwamitin bincike da ya kafa don nazarin matsalolin da suka faru a cikin ɗaukar malamai da hukumar NSTSC ta yi kwanan nan.

Wane mataki za a ɗauka?

A cewarsa, rashin gaskiyar da aka gano a cikin shirin ɗaukar malamai ya tilasta shi mika batun ga hukumomin tsaro, musamman duba da cewa an karɓi kuɗi daga masu neman aikin a matsayin toshiyar baki don ba su takardun aiki.

"Wadannan mutane dole mu mika su ga hukumomin tsaro, saboda wannan matsala ta fi ƙarfin ɓangaren gudanarwa."
"Batun su karɓar kuɗi daga hannun mutane, ni kaina ba ni da ikon yanke hukunci akai. Ya dace hukumomin tsaro su shiga cikin lamarin domin ganin an mayarwa da waɗannan matasan kuɗinsu."
Gwamnan ya nuna takaici kan binciken da kwamitin ya yi, yana mai cewa jami’an da aka dakatar ba su yi wa jihar adalci ba saboda sun wuce iyakar da aka ba su wajen ɗaukar ma’aikata.

Kara karanta wannan

Gwamnan Zamfara ya yi alhinin rasuwar Almajirai a gobara, ya fadi matakin ɗauka

"Mun amince a ɗauki malamai 1,000 ne kawai, amma su sun je sun ɗauki 3,277. Yanzu ta yaya za a iya ɗaukar nauyin waɗannan malamai a yau a jihar Nasarawa? Daga ina za a samo kuɗin biyansu? Ina za a tura su aiki?"

- Gwamna Abdullahi Sule

Gwamna Sule ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta amince da irin wannan cin hanci da rashawa ba, kuma duk wanda aka samu da hannu a cikin lamarin zai fuskanci hukunci daga hukumomin tsaro.

Gwamna Sule ya yi kora a gwamnatinsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya runtuma kora a gwamnatinsa.

Gwamna Abdullahi Sule ya kori dukkanin masu riƙe da muƙaman siyasa a gwamnatinsa a wani shiri na yin garambawul.

Korar masu riƙe da muƙaman siyasan dai na zuwa ne ƴan kwanaki bayan gwamnan ya rushe majalisar zartarwar jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng