Ana Fama da Tsadar Abinci, Gwamnati Ta Yi Maganar Kayyade Farashin Kayayyaki
- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ba ta da iko kan ƙayyade farashin kayayyaki, sai dai tabbatar da gaskiya a harkar kasuwanci
- Dakta Tunji Bello, shugaban FCCPC ya ce aikin hukumar shi ne kare haƙƙin masu amfani da kayayyaki da tabbatar da adalci a kasuwa
- Gwamnatin tarayya ta yi kira ga masu amfani da kayayyaki da su rika mika ƙorafe-ƙorafensu idan aka take musu haƙƙi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar kula da gasar kasuwanci da kare hakkin masu amfani da kayayyaki (FCCPC) ta ce ba ta da ikon ƙayyade kudin kaya ko ayyuka.
Shugaban Hukumar, Dakta Tunji Bello, ya bayyana cewa ƙayyade farashi ba ya daga cikin ayyukan da aka shar'antawa FCCPC a dokar kasa.

Asali: Facebook
FCCPC ta yi bayani kan tsarin ayyukanta
Dakta Tunji Bello ya yi wannan bayani ne a wata hira ta kai tsaye da aka yi da shi a wani gidan talabijin a karshen makon nan, inji rahoton The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ya ce babban aikin hukumar FCCPC shi ne kare haƙƙin masu amfani da kayayyaki da ayyuka a Najeriya.
Dakta Bello ya ce sauya sunan hukumar daga cibiyar kare masu amfani da kayayyaki (CPC) zuwa FCCPC ya ba ta damar yin aiki da doka sosai.
'Ba aikinmu ba ne kayyade farashi' - FCCPC
A cewarsa, hakan ya bai wa hukumar ikon tabbatar da gaskiya da adalci a kasuwanni tare da hana rashin gaskiya a harkar kasuwanci.
"Idan ana magana kan farashin kayayyaki, to aikinmu shi ne tabbatar da cewa farashin ya dogara ne ga bukata da wadatar kayan.
"Ba mu da ikon cewa ga farashin da dole 'yan kasuwa su sayar da kaya, domin mu ba hukumar kula da farashin kaya ba ce."
- Dakta Tunji Bello.
Ya yi kira ga 'yan Najeriya da su rika mika koke-kokensu idan an take musu haƙƙi ta hanyoyin da aka tanada don karɓar ƙorafe-ƙorafe.

Kara karanta wannan
'Gwamnati ta kawo sabon haraji da zai jawo tashin farashi,' Saraki ya tono magana
FCCPC ta gano masu jawo tsadar abinci
A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar FCCPC ta gano wasu masu sayar da kayan abinci suna boye amfanin gona don haddasa tsadar kaya.
Shugaban hukumar FCCPC, Dakta Tunji Bello, ya ce wannan boye kaya yana jawo karancin abinci da hauhawar farashi a kasuwanni.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng