An Dakatar da Basarake kan Zargin Sara Maraya da Adda, Dagaci Ya Yi Magana

An Dakatar da Basarake kan Zargin Sara Maraya da Adda, Dagaci Ya Yi Magana

  • Hukumomi a Gombe sun dakatar da Dagacin Kagarawal a jihar, Usman A. Bello, bisa zargin saran wani maraya da adda har sau bakwai
  • Hukumomin sun dauki matakin ne domin samun damar kammala bincike kan zargin da dagacin kafin yanke hukuncin da ya kamata
  • Marayan mai shekara 15, Adamu Muhammad, ya samu raunuka, amma asibiti sun ki karbarsa saboda rashin kudi, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce
  • Dagacin ya musanta zargin, yana cewa wasu matasa ne suka shiga gidansa da makamai, shi kuma ya kwace adda daga hannunsu don kare kansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Gombe - Hukumomin a jihar Gombe sun dauki mataki kan wani dagaci da ake zargin ya sassara maraya da adda.

An dakatar da Dagacin unguwar Kagarawal a Gombe, Usman A. Bello, bisa zargin saran marayan mai shekara 15 da adda har sau bakwai.

Kara karanta wannan

Sabon limamin Abuja ya yi nasiha mai zafi ga malamai masu jifan juna ta intanet

Ana ci gaba da bincike bayan dakatar da basarake kan zargin saran maraya
Hukumomi a Gombe sun dakatar da Dagacin Kagarawal kan zargin saran matashi. Hoto: Isma'ila Uba Misilli, Ibrahim Yinsa Ib Goro.
Asali: Facebook

An dakatar da Dagaci a kauyen Gombe

Hukumomi sun dauki wannan mataki ne domin ba da damar gudanar da cikakken bincike kan lamarin kafin yanke hukunci, cewar Aminiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ruwaito cewa marayan, Adamu Muhammad, ya samu munanan raunuka sakamakon sarar da aka yi masa.

Amma kuma likitoci sun ki karbarsa a asibiti saboda rashin kudi, lamarin da ya haddasa ce-ce-ku-ce.

Daga bisani, an tabbatar cewa hukumomi ne a karamar hukuma suka dauki nauyin jinyarsa.

Abin da Dagaci ya ce kan zargin saran maraya

A martaninsa, Dagacin ya musanta zargin cewa shi ya sare yaron yana mai tabbatar da cewa kare kansa ya yi.

Dagacin ya bayyana cewa wasu matasa dauke da makamai sun kutsa gidansa cikin dare, shi kuma ya kwace adda daga hannunsu don kare kansa.

Hukumomi na ci gaba da bincike kan lamarin domin gano bakin zaren da kuma daukar matakin da ya dace.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bindiga sama da 100 suka taru wajen sace Janar Tsiga a Katsina

Legit ta ji ta bakin wasu daga yan yankin

Daya daga cikinsu, Muhammad Salisu ya tabbatar da cewa yaron da ake magana a kai yana asibiti.

Sai dai ya ce ba kamar yadda ake yadawa ba, yaron ne ya je gidan Dagacin da tsakar dare wanda hakan ya sanya zargi.

"Tabbas Dagacin ma ya musanta abin da ake zarginsa a kai da cewa yana kokarin kare kansa ne."

- Cewar Salisu

'Abin da ya faru kan zargin sara maraya' - Maraya

A baya, kun ji cewa yayin da ake zargin wani dagaci da sassara matashi kan zargin sata a gidansa a unguwar Kagarawal a jihar Gombe, basaraken ya yi magana.

Dagacin ya musanta labarin inda ya ce yaron ya zo yi masa sata ne inda suka yi artabu sosai kafin kwace wukar hannunsa domin kare kansa saboda fargabar abin da zai biyo baya.

Matashin mai suna Adamu Muhammad ya zargi dagacin da ji masa raunuka wanda yanzu yake kwance a gadon asibiti yayin da ake ci gaba da bincike.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.