Gwamnan Arewa Mai Sukar Kudirin Harajin Tinubu Ya Sauya Ra'ayi, Ya Fadi Dalili
- Gwamnan jihar Nasarawa wanda yana ɗaya daga cikin masu sukar ƙuɗirin harajin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, ya sauya ra'ayi
- Abdullahi Sule ya bayyana cewa ya suya ra'ayinsa ne kan sukar ƙudirorin saboda an magance damuwar da yake da ita a kansa
- Gwamnan ya nuna cewa tun da farko baya son a amince da ƙudirin harajin ne a asalin tsarin da mai girma Bola Tinubu ya fito da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana dalilin da ya sa ya sauya ra’ayinsa kan ƙudirin gyaran haraji na gwamnatin Bola Tinubu.
Gwamna Sule ya bayyana cewa ya sauya ra'ayi ne nan ƙudirin da ya haifar da ce-ce-ku-ce, saboda an magance damuwar da yake da ita a kansa.

Asali: Twitter
Gwamna Sule, wanda ya kasance ɗaya daga cikin shugabannin Arewa masu nuna adawa da ƙudirin tun farko, ya bayyana hakan ne yayin wata hira a shirin Politics Today na tashar Channels TV.

Kara karanta wannan
Wasu ƴan siyasa na neman canza sunayen talakawan da za a ba tallafin kudi a Najeriya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa Gwamna Sule ya sauya ra'ayi?
Ya bayyana cewa adawarsa ba ta kasance da ra’ayin gyaran haraji ba, amma tana da nasaba da abubuwan da ke cikin ƙudirin.
A cewarsa, burin da aka sa a gaba shi ne a tabbatar da cewa an tattauna kan ƙudirin sosai kafin a yanke wani hukunci.
"Mun cimma burinmu, kuma wannan ne dalilin da ya sa a yau nake magana daban. Ina magana daban saboda burin da muke son cimmawa ya riga ya tabbata."
“Mun so a tattauna ƙudirin sosai kuma ka da amince da shi a asalin tsarin da aka fito da shi.
"Yanzu, akwai damar sake dubawa, kuma ina yabawa majalisar wakilai, musamman shugaban majalisar, saboda yadda suka tafiyar da batun."
- Abdullahi Sule
Gwamna ya yaba ƙudirin harajin Bola Tinubu
Gwamnan ya nuna gamsuwarsa da yadda ƴan majalisa, musamman na majalisar wakilai da shugaban ta, suke tafiyar da ƙudirin a yanzu.
Ya ce damuwar da ya nuna tare da wasu mutane ta sa an sake nazarin ƙudirin sosai.
Gwamna Sule ya kuma bayyana cewa irin wannan tattaunawa tana da muhimmanci, wajen tabbatar da cewa duk wani ƙudiri da zai shafi jama’a an aiwatar da shi cikin adalci da kuma la’akari da buƙatun jama’a.
Wannan canjin matsayi ya nuna cewa ana iya samun fahimtar juna dan aka duba dukkanin ɓangarori dama su tattauna da kuma bayyana ra’ayinsu kan duk wani al’amari da ya shafi jama’a.
Ƙudirin harajin dai ya sha suka sosai musamman daga Arewacin Najeriya inda ake tunanin cewa zai yi wa yankin illa.
Gwamna Sule ya yi garambawul a gwamnati
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi zazzaga a gwamnatinsa bayan ya yi wani ƙwarya-ƙwaryar garambawul.
Gwamna Abdullahi Sule ya kori sakataren gwamnatin jihar (SSG) daga muƙaminsa tare da rusa majalisar zartaswar jihar gaba ɗayanta.

Kara karanta wannan
"Na yi rashin babban amini," Buhari ya yi ta'aziyyar mutuwar abokinsa na kud da kud
Gwamnan wanda bai bayyana dalilin ɗaukar matakin ba, ya kuma kori dukkanin hadimansa da kwamishinonin da ke cikin gwamnatinsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng