Atiku Ya Yi wa Gwamnatin Tinubu Shagube a kan Batar da Kasafin Kudi
- Atiku Abubakar, ya nemi gwamnati ta tabbatar da cewa kuɗin da aka ware wa fannin kiwon lafiya ba su shiga hannun wasu tsirarun mutane ba
- Ya ce wajibi ne gwamnati ta samar da ingantaccen tsari na bincike da bibiyar yadda ake kashe waɗannan kuɗaɗe domin sa ido a kan inda aka zuba su
- Atiku ya ce rashin fayyace yadda za a kashe wannan kuɗi, wanda yawancinsa bashi ne daga ƙetare, babbar matsala ce ganin cewa sai an biya kudaden
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya gargadi Gwamnatin Tarayya da kada ta bari dala biliyan 1.07 da aka ware wa fannin kiwon lafiya a kasafin kuɗin 2025 su tafi a banza.
Ya ce babu dalilin da zai sa wannan kasafi ya afka cikin matsalolin da aka taba ji a baya, irin su zargin cewa macizai, tururuwa, ko birai sun cinye kuɗaɗen gwamnati.

Asali: Facebook
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ɗan takarar shugaban ƙasar na 2023 ya bukaci a gina ingantaccen tsari don tabbatar da cewa an yi amfani da kuɗaɗen wajen inganta ayyukan lafiya, ba wai su ɓace a cikin wasu munanan hanyoyi ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ya bukaci bayyana ayyukan gwamnati
Daily Trust ta ruwaito Atiku Abubakar ya jaddada buƙatar kafa tsarin da zai sa a bibiyi yadda za a kashe waɗannan kuɗaɗe domin tabbatar da amfaninsu ga al’umma.
Ya ce:
"Saboda haka, wajibi ne Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa an samar da ingantaccen tsari na bincike da bayyananniyar tafiyar da dala biliyan $1.07 da aka ware wa fannin kiwon lafiya."
Atiku ya soki gwamnati kan boye bayanai

Kara karanta wannan
"Shirin gwamnati ya gaza, " Tsohon gwamnan APC ya fito da matsalolin mulkin Tinubu
Atiku Abubakar ya soki Gwamnatin Tarayya kan rashin bayyana cikakken bayani kan yadda take shirin kashe kudaden da aka ware a fannin kiwon lafiya.
Ya ce kamata ya yi gwamnati ta hanzarta zuba jari a kiwon lafiya, musamman a matakin farko domin samar da ingantattun tsarin samun lafiya ga ‘yan Najeriya.
Atiku ya ce:
"Mun karanta cewa Gwamnatin Tarayya na shirin kashe dala biliyan $1.07 a bangaren kiwon lafiya na matakin farko.
Wannan adadi yana nufin ƙarin fiye da tiriliyan 2.48 da aka riga aka tanada wa fannin lafiya a daftarin kasafin kuɗi na farko.
"Abin da ke daure kai shi ne, gwamnatin ta bayyana cewa yawancin wannan kuɗi daga basussukan ƙetare ne, tare da ɗan gudunmuwa daga wata ƙungiyar tallafi ta ƙasa da ƙasa.
"A takaice, Najeriya za ta biya wannan bashi, don haka ya zama wajibi ga ‘yan ƙasa su san cikakken bayani game da shi. Kuma dole ne a fayyace yadda za a kashe kuɗin a wata doka da za ta bayyana tsare-tsaren kashe su."
Atiku ya soki gwamnati gabanin zaben 2027
A baya, kun ji cewa tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya caccaki shugaba Bola Tinubu, yana mai zarginsa da rashin tsari mai kyau wajen karfafa dimokuradiyya a Najeriya.
A wata sanarwa da hadiminsa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya fitar, Atiku ya zargi Tinubu da rashin shiri ko wata manufa ta inganta tsarin dimokuradiyya a ƙasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng