Duniya ba Tabbas: An Sake Rashin Babban Malamin Musulunci a Najeriya, Atiku Ya Jajanta

Duniya ba Tabbas: An Sake Rashin Babban Malamin Musulunci a Najeriya, Atiku Ya Jajanta

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi jimamin mutuwar babban malamin Musulunci a Adamawa
  • Wazirin Adamawa ya yi ta'aziyyar bayan mutuwar Sheikh Ibrahim Abubakar Daware wanda ya ba da gudunmawa sosai
  • Tsohon dan takarar shugaban kasa ya ce marigayin ya taba shugabantar Firyanul Islam Adamawa kuma fitaccen malami ne
  • Ya yi addu’ar Allah ya gafarta masa, ya ba iyalansa da abokansa haƙuri, kuma ya ba shi matsuguni a cikin Jannatul Firdausi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Yola, Adamawa - Tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya jajanta da aka yi rashin malamin Musulunci.

Atiku ya mika ta’aziyyarsa bisa rasuwar Sheikh Ibrahim Abubakar Daware, malamin addinin Musulunci a Jihar Adamawa.

Atiku ya jajanta bayan rasuwar malamin Musulunci a Adamawa
Malamin Musulunci a Adamawa, Sheikh Abubakar Daware ya rasu. Hoto: @atiku.
Asali: Twitter

Atiku ya yi ta'azziya bayan rasuwar malami

Atiku ya tura sakon ta'azziyar a yau Juma'a 7 ga watan Janairun 2025 a shafinsa na X inda ya ce an yi babban rashi.

Kara karanta wannan

'Shi zai iya gyara Najeriya': Dan PDP ya roki Kwankwaso, Obi su hade da Atiku Abubakar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce marigayin ya kasance tsohon shugaban Firyanul Islam Adamawa.

Atiku ya ce malamin ya kuma kasance babban malami ne a fannin fikihu na Sufaye a Najeriya.

Daga bisani ya yi addu'ar Allah ya ba danginsa da abokansa haƙurin jure wannan babban rashi da suka yi.

Ya roki Allah Maɗaukakin Sarki ya gafarta masa zunubansa, ya rahamshe shi, ya ba shi matsuguni a cikin Jannatul Firdaus.

Atiku ya yi ruwan addu'o'i ga marigayin

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un, Ina mika ta’aziyyata ta bisa rasuwar Sheikh Ibrahim Abubakar Daware, fitaccen malamin addinin Musulunci a Jihar Adamawa.
"Marigayin tsohon shugaban Firyanul Islam a Adamawa ne kuma babban malami a fannin fikihu na Sufaye a Najeriya, Allah ya ba iyalansa da abokansa haƙuri.
"Ina roƙon Allah Maɗaukaki ya gafarta masa zunubansa, ya rahamshe shi, ya ba shi matsuguni a cikin Jannatul Firdaus. Ameen."

- Atiku Abubakar

Kara karanta wannan

2027: Kashim Shettima ya fadi yadda ya ke mu'amalantar Atiku a bayan fage

Tsohon hadimin Atiku ya yi bankwana da duniya

A baya, mun ba ku labarin cewa hadimin tsohon mataimakin shugaban kasa, Hon. Shima Ayati ya rasu a Makurdi bayan gajeriyar rashin lafiya.

Ayati ya yi aiki tare da Atiku Abubakar a lokacin mulkin Olusegun Obasanjo kuma ya jagoranci kwamitin tallafin Zaki Biam a 2003.

Marigayin dan asalin karamar hukumar Ukum ta jihar Benue, ya bar siyasa domin mayar da hankali kan kasuwancinsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.