Boko Haram Ta Bullo da Sabuwar Dabarar Kashe Bayin Allah, An Hallaka Mutane a Borno
- Wasu abubuwan fashewa sun tarwatse a hanya, tare da hallaka mutane biyu a kan hanyarsu zuwa kasuwar Garkida a Adamawa
- 'Yan sanda sun tabbatar da harin, sun ce mota dauke da yan kasuwar ta taka bam din da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka dasa
- Wani dan uwa wanda abin ya shafa, ya ce 'yan ta’adda na dasa bama-bamai a hanyoyin karkara da dare, a wani sabon salon kai hari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno - Mutane biyu sun rasa rayukansu sakamakon fashewar abubuwan fashewa (IEDs) da 'yan ta'addan Boko Haram suka dasa a hanya yayin da wasu matafiya ke kan hanyarsu zuwa kasuwa a jihar Adamawa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Borno, ASP Kenneth Daso da ya tabbatar da harin ya ce mutunen na kan hanyarsu ta zuwa kasuwar Garkida a jihar Adamawa.

Asali: Original
A labarin da ya kebanta ga Daily Trust, harin ya faru ne a ranar Talata a tsakanin kauyukan Harang da Jibhuhwui na karamar hukumar Hawul a jihar Borno, da ke kan hanyar zuwa kasuwar Garkida a jihar Adamawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya bayyana cewa, motar da matafiyan ke ciki ta taka IED din, wanda ya fashe, tare da hallaka mutane biyu a wurin.
'Yan sanda sun tabbatar da harin Boko Haram
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Borno, ASP Kenneth Daso, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa mutane shida ne ke cikin motar a lokacin fashewar.
Ya ce:
"Ana zargin 'yan ta'addan Boko Haram ne suka dasa bam din, kuma wata mota kirar pick-up da ke dauke da matafiya zuwa kasuwar Garkida ta taka shi, wanda ya haddasa fashewa.
"Adama Yakubu mai shekara 25 ta mutu nan take, yayin da sauran fasinjojin aka garzaya da su asibiti don samun kulawa."

Kara karanta wannan
Dambarwar Albany da abubuwa 4 da suka ta da kura a kafofin sadarwa a Arewacin Najeriya
'Yan sanda na binciken harin Borno
ASP Daso ya kara da cewa rundunar 'yan sanda tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro na aiki ba dare ba rana don tabbatar da tsaron yankin.
Haka kuma ya ce su na kokarin dakile duk wani barazana ga zaman lafiya, yayin da ya bukaci al’ummar yankin da su rika bayar da rahoton duk wani motsi ko ayyukan da ake zargi.
Mazauna Borno sun koka da harin Boko Haram
Wani dan uwa na daya daga cikin wadanda lamarin ya shafa, ya ce 'yan ta'addan sun mayar da al'ummomin biyu wuraren kai hare-haren IED da suke dasawa cikin dare a hanyoyin karkara.
Ya roki hukumomin tsaro da su tura karin jami’an tsaro da kayayyakin aiki zuwa yankin, yana mai cewa hare-haren 'yan ta’adda a yankunan Damboa, Chibok da gefen dajin Sambisa na kara tsananta.
'Yan Boko Haram sun kai hari a jihar Borno
A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan ta'addan Boko Haram sun kai hari ofishin 'yan sanda na Nganzai, a garin Gajiram, karamar hukumar Nganzai ta jihar Borno.
A yayin wannan harin, an rasa rayukan jami'an 'yan sanda biyu, yayin da wani jami'i ya samu munanan raunuka a lokacin da yan ta'addan suka jefa gurneti ga ofishin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng