Gwamnonin Arewa Sun Hana Amfani da Turanci a Matsayin Yaren Koyarwa a Makarantu?

Gwamnonin Arewa Sun Hana Amfani da Turanci a Matsayin Yaren Koyarwa a Makarantu?

  • Ana ta yada jita-jitar cewa gwamnonin Arewa sun yanke shawarar cire Turanci daga matsayin harshen koyarwa a makarantu
  • Bincike ya nuna babu wata sanarwa daga gwamnonin da ke nuna cewa sun yanke shawarar daina amfani da Turanci a makarantu
  • Gwamna Umar Bago ne ya bayar da shawarar amfani da Hausa domin haɓaka karatu, amma ba a ɗauki hakan a matsayin doka ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Neja - Ana zargin cewa gwamnonin Arewa sun yi watsi da Turanci a matsayin harshen koyarwa a makarantun Arewacin kasar nan.

Jita jitar da ta fara yaduwa a Facebook ta ce gwamnonin Arewa sun yanke shawarar canja harshen koyarwa daga Turanci zuwa wani yare na gida.

Rahoto ya yi bayani game da zargin daina amfani da harshen Turanci a makarantun Arewa
Babu gaskiya a zancen daina amfani da Turancin a matsayin harshen koyarwa a Arewa. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Ana zargin daina koyarwa da Turanci a Arewa

Rahoton Africa Check ya nuna cewa an kawo Turanci Najeriya ne ta hannun ‘yan kasuwa da mishanoni na Birtaniya a ƙarnuka na 16 da 17.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya gana da tsohon gwamnan APC, an yi hasashen shirin tumbuke Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A makarantu na mishanoni, an mai da Turanci mahimmin fanni na koyarwa yayin da daga bisani ya zama harshen koyarwa a hukumance.

Shin wannan zargi gaskiya ne? Mun bincika domin gano sahihancin batun.

Har yanzu Turanci ne yaren koyarwa a Arewa

Tun bayan samun ‘yancin kai a 1960, Najeriya ta rungumi Turanci a matsayin harshen bai daya don haɗin kai da sauƙaƙe mulki.

Har yanzu, Turanci ne babban harshen koyarwa a makarantu, kuma doka ta amince da shi tare da Hausa, Yoruba da Igbo.

Binciken shafin Dubawa bai gano wata sahihiyar majiya da ta tabbatar da wannan matsaya daga gwamnonin Arewa ba.

An canja ma'anar shawarar Gwamna Bago

Abin da aka gano, shi ne jawabin Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja a lokacin wani taron marubuta.

Gwamna Bago ya ba da shawara cewa a ɗauki Hausa a matsayin yaren koyarwa domin taimakawa yara wajen fahimtar darussa da haɓaka shiga makaranta.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bindiga sama da 100 suka taru wajen sace Janar Tsiga a Katsina

Duk da cewa rahotanni sun wallafa hakan, amma babu wata hujja cewa gwamnonin Arewa sun mayar da hakan doka, sabanin ikirarin jita-jitar Facebook.

'Da Turanci muke koyarwa' - Nura Mailafiya

Da Legit Hausa ta tuntubi wani malamin makaranta a Katsina, Nura Lawal Mailafiya, ya shaida mana cewa da Turanci suke koyarwa a makarantunsu.

"Ba mu samu wani umarni na cewa mu koyar da harshen Hausa ba, da turanci muke koyar da dalibai gaskiya.

"Koyarwa da harshen Hausa na da amfaninsa, to amma dukkanin littattafai da hanyar koyarwar an tsara su ne a kan Turanci.

"Kafin fara koyarwa da Hausa, ma'aikatar ilimin jihohi da ta tarayya za su yiwa tsarin koyarwa garambawul, a samar da littattafan Physic, Chemistry, Geography, duk na Hausa."

Malam Nura ya ce koyarwa da Hausa zai karfafawa yara gane abin da ake koyar da su, inda ya nemi gwamnati ta sake waiwayar matsayar Gwamnatin Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Mummunar gobara ta tashi a makarantar allo, an samu asarar rayukan dalibai

Za a fara amfani da harshen 'uwa' a makarantu

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta amince a koyar da daliban firamare da harsunan gida.

An rahoto cewa Najeriya na da harsuna sama da 625, kuma gwamnati ta ce za a yi amfani da su wajen koyar da yara a matakin firamare.

Gwamnatin tarayya ta ce aiwatar da wannan tsari zai ɗauki lokaci, amma za ta tabbatar da komai ya gudana cikin tsari da kyakkyawan shiri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.