FG Ta Wajabta Fara Koyar Da Daliban Firamare Da Harsunan Hausa, Yarbanci Da Igbo A Makarantun Najeriya

FG Ta Wajabta Fara Koyar Da Daliban Firamare Da Harsunan Hausa, Yarbanci Da Igbo A Makarantun Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za a fara koyar da daliban frimare na Najeriya da harsunan 'uwayensu' a makarantu
  • Ministan Ilimi, Adamu Adamu ne ya sanar da hakan yayin tattaunawa da ya yi da manema labarai bayan taron majalisar zartarwa, FEC
  • Adamu ya ce gwamnati za ta samar da tsarin koyarwar kuma za ta dauki sabbin malamai da za su taimaka wurin aiwatar da tsarin

FCT Abuja - Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce daga yanzu za a fara amfani da harsunan dalibai wurin koyar da su a makarantun firamari 1 zuwa 6 a kasar, The Punch ta rahoto.

Adamu Adamu, ministan ilimi, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da ya ke magana da manema labarai bayan kammala taron FEC.

Makaranta
Gwamnatin Najeriya Ta Wajabta Koyarwa Da Harshen Uwa A Makarantun Firamare 1 Zuwa 6. Hoto: @thecableng.
Asali: Twitter

Adamu ya ce gwamnatin tarayya ta fahimci cewa aiwatar da tsarin zai zo da kallubale, tana mai cewa za a rika gwamutsa harsunan daliban da turanci daga kananan ajin firamare.

Kara karanta wannan

A Karshe Gwamnatin Tarayya Tayi Magana Game da Kara Farashin Fetur Zuwa N400

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Harshen mahaifiya shine harshen da aka fara koya wa mutum lokacin yana karamin yaro.

Ya ce duk da cewa tsarin ya fara aiki a hukumance, FG za ta samar da kayan koyarwa tare da daukan malamai kwararru domin aiwatar da shi, rahoton The Cable.

Harshen da mutane suka fi amfani da shi a yanki shine makaranta za ta yi amfani da shi - Adamu

Ya kara da cewa harshen da mafi yawan mutanen yanki ke magana da shi ne zai zama harshen da za a rika amfani da shi a makarantun

Adamu ya koka da cewa harsuna da yawa suna dab da bacewa, yana mai cewa FG tana son tabbatar da cewa harsuna da al'addun ba su bace ba.

Dukkan harsunan Najeriya suna da muhimmanci kuma za a rika basu daraja daya, in ji shi.

Kara karanta wannan

Daga karshe, za a fara koyar da dalibai da harshen Hausa a makarantun firamare

Ra'ayoyin wasu malaman firamare da karamar sakandare kan koyar da dalibai da 'harshen uwa'

Legit.ng Hausa ta tattauna da wasu malaman makaranta domin jin ra'ayinsu kan umurnin da gwamnatin tarayya ta bada na wajabta koyarwa da harsunan Najeriya.

Malam Naziru Dalha Taura, malami a makarantar gwamnati ta 'Day Science Secondary School, Dutse' ya ce baya goyon bayan matakin da ya bayyana a matsayin ci baya.

Ya ce Najeriya kasa ce mai mutane masu harsuna mabanbanta don haka turancin shine harshen da suke taruwa kansa don fahimtar juna.

Cikin tsokacin da ya yi game da batun ya ce:

"Gaskiya ci baya, saboda Najeriya ta riga ta zabi turanci a matsayin harshe da ake amfani da shi a hukumance, kuma idan aka kwatanta igancin turanci na Najeriya bai kai na kasashen Afirka irinsu Ghana da Liberia da sauransu.
"Ko da ake fara koyarwar daga firamare mutanen mu da kyar suke iyawa, yanzu kuma an ce za a dena koyarwa daga tushe.

Kara karanta wannan

Dalilin Watsi da Dokar Haramtawa K/Napep Amfani da Manyan Tituna Bayan Kwana 1

"Dama cikin malaman akwai da dama wadanda ba iya turancin suka yi ba, musamman a makarantun firamari, wannan matakin zai ba su damar zullewa."

Ya cigaba da cewa:

"Yaushe ake son daliban su koya turancin? Idan wasu daliban mu a yanzu suna gama makarantun gaba da sakandare ba tare da sun iya turanci mai kyau ba, yaya abin zai kasance idan an fara koyarwa harsunan uwa.
"Najeriya kasa ce mai mutane masu harsuna daban-daban, idan aka mayar da hankali wurin koyarwa da harsunan uwa, kuma turancin ba a iya shi ba sosai, ta yaya za su fahimci juna idan sun hadu?"

Hakazalika, malamar makarantar firamari a Kawo Kaduna, wacce ta nemi a sakayya sunanta, ta ce bata goyi bayan wannan tsarin ba domin a ganinta daliban za su samu kallubale idan sun tafi manyan aji, ko rubuta jarrabawar kammala sakandare ko zuwa karatu kasashen waje.

Ta ce:

"Gaskiya bana goyon bayan tsarin nan, dama da yaya ake fama da daliban yanzu kuma idan an koma harshen uwa ta yaya za su yi idan sunyi gaba a karatu ko sun fita kasar waje."

Kara karanta wannan

"Ba Bayan Gida, Babu Girki": Dan Najeriya Ya Gina Bandaki Mai Samar Da Iskar Das Don Girki Da Wutar Lantarki

A bangarenta, Hafsat Ibrahim, wata malama a 'Dalet Girls Secondary School Kaduna' ta ce a ra'ayin kanta tana goyon bayan tsarin na gwamnati wanda ta ce zai taimaka dalibai su rika fahimtar abin da ake koyar da su.

Malamar, wacce ke koyarwa a ajin karamar sakandare na 1 da biyu ta ce tun kafin wannan umurnin dama a wasu lokutan suna gwamutsawa da harshen hausa idan ba hakan ba daliban ba su fahimtar komai. Amma kuma ta ce iya magana da turanci zai musu wahala.

Kalamanta:

"Wannan tsarin zai taimaka wa dalibai wurin kara fahimta amma kuma ba dole bane su iya magana da harshen turancin sosai.
"Duk da dai daliban na yanzu masu tasowa sun fi na baya kwazon fahimtar turancin."

Za a kashewa Jami'ar UDUS Naira Biliyan 3.26, In Ji Ministan Ilimi, Adamu Adamu

A wani rahoton, Adamu Adamu, ministan ilimi na Najariya ya ce an ba wa kamfanin Amis Construction Nigeria Ltd. kwangilar zagaye Jami'ar Usmanu DanFodio da ke Sokoto.

Daily Trust ta rahoto cewa an amince da bada kwangilar ne yayin zaman majalisar koli ta kasa, FEC, da aka yi a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel