Nasarorin da aka Samu a Cibiyar Darul Hadith Shekaru 11 bayan Rasuwar Albani Zariya
- Cibiyar Daarul Hadeethis Salafiyyah da ke Zariya ta fitar da nasarorin da ta samu shekaru 11 bayan rasuwar Auwal Albani da ya assasata
- Daga cikin nasarorin da aka cimma akwai biyan bashin N60m, ƙara yawan ɗalibai zuwa 1500 da kafa tashar talabijin nan ta Albani TV
- Manyan shugabannin cibiyar sun gode wa Allah da duk waɗanda suka ba da gudunmawa wajen cigaban Daarul Hadeethis Salafiyyah
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Cibiyar Daarul Hadeethis Salafiyyah da ke Zariya ta bayyana nasarorin da ta samu a cikin shekaru 11 da suka gabata bayan rasuwar Sheikh Muhammad Auwal Albani Zariya.
Shugabannin makarantar sun bayyana cewa an cimma wadannan nasarori ne ta hanyar haɗin kai da sadaukar da kai daga dukkan sassan cibiyar.

Kara karanta wannan
Matakin da majalisa ta dauka kan zargin Janar Tchiani game da Lakurawa, tana kokwanto

Asali: Facebook
Sanarwar ta fito ne daga Daraktan cibiyar, Dr Kabir Abubakar Amin (Asgar) tare da tsohon daraktan cibiyar, Farfesa Abdurrafi’ Abdulganiyyi a wani sako da suka wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nasarorin da cibiyar Albani Zariya ta samu
Bayan rasuwar marigayi Sheikh Muhammad Auwal Albani, Daarul Hadeethis Salafiyyah ta ci gaba da tafiya bisa turbar da ya kafa ta,
Cibiyar ta samu damar biyan bashin N60m da marigayi Sheikh Albani ya bari, wanda yawanci shi ya rubuta da hannunsa.
Haka zalika, an ƙara yawan ɗaliban makarantar daga ƙasa da 500 zuwa 1500, yayin da adadin ma’aikata ya ƙaru daga ƙasa da 100 zuwa 300.
Akwai kuma karin dakunan karatu daga 15 zuwa 50, ofis daga 2 zuwa 15, da kuma ƙarin dakin gwaje-gwaje daga 1 zuwa 5.
Sababbin ayyuka da shirye-shiryen Darul Hadith
Daga cikin sababbin abubuwan da aka samar a cikin shekarun akwai kafa wurin kula da lafiya da kuma aza tubalin ginin asibitin Albani.

Kara karanta wannan
Matasan Arewa sun fadi sunayen 'yan siyasa 3 da ke shirin ruguza gwamnatin Tinubu
Haka zalika, an gina masallacin Juma’a mai iya daukar mutane 1000 a lokaci guda, tare da kafa tashar Albani TV don yada ilimi da wa’azi.
Makarantar ta kuma samu ƙarin filaye biyu a bayan ɓangaren mata na makaratun firamare da kasa da firamare domin fadada cibiyar.
An kuma kafa kwamitin kula da marayu, inda aka samar da tallafin karatu ga ɗalibai 16 da ke karatu a jami’o’i daban-daban a Najeriya da ƙetare.
Godiya da fatan alheri ga jama'a
Shugabannin Daarul Hadeethis Salafiyyah sun bayyana matuƙar godiyarsu ga Allah SWT bisa nasarorin da aka samu a cikin shekaru 11 da suka gabata.
Sun kuma yi addu’ar Allah ya cigaba da kare cibiyar da duk masu bada gudunmawa domin cigaban makarantar.
Haka zalika, sun yi addu’ar Allah ya gafarta wa marigayi Sheikh Muhammad Auwal Albani tare da sanya shi cikin Aljannar Firdausi.

Kara karanta wannan
Tinubu ya ji takaicin konewar almajirai, ya ba da umarnin dakile gobara a tsangayu
Sun jaddada cewa za su ci gaba da kokarin tabbatar da inganta harkokin ilimi, jin daɗin ɗalibai da cigaban cibiyar gaba ɗaya.
Ramadan: Guruntum ya yi nasiha kan sulhu
A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum ya yi nasiha ga al'ummar Musulmi yayin da watan Ramadan ke karatowa.
Malamin ya bukaci duk masu gaba a tsakaninsu da su yi sulhu domin a cewarsa, hakan zai iya yin tasiri a kan azumin da za su yi a Ramadan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng