Tinubu Ya Ji Takaicin Konewar Almajirai, Ya ba da Umarnin Dakile Gobara a Tsangayu
- Wata gobara da ta tashi da daddare a wata makarantar Tsangaya a Kaura Namoda, Jihar Zamfara, ta yi sanadin mutuwar yara 17
- Gobarar, wacce ta tashi a makwancin daliban da tsakar dare, ta kuma jikkata wasu almajira guda 15 da a yanzu suke karbar magani
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci makarantu da su bi ka’idojin tsaro domin kare dalibai daga hadurran gobara nan gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Zamfara - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya jajanta wa iyaye, da dangin wadanda suka rasa ‘yan uwansu a gobarar da ta tashi a wata makarantar tsangaya a Kaura Namoda da ke jihar Zamfara.
Bola Tinubu ya mika ta’aziyyarsa a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Laraba.

Asali: Facebook
A cikin wani sako da aka wallafa a shafin X na Ofishin Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Sadarwa, Tinubu ya jaddada bukatar daukar matakan hana afkuwar irin wannan gobara a gaba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gobarar da ta tashi da daddare a tsangaya , kuma ta yi sanadin mutuwar yara 17 tare da jikkata wasu dalibai 15.
Bola Tinubu ya ba da umarnin dakile gobara
Jaridar Punch ta ruwaito cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bada umarni ga makarantu da su fi mayar da hankali kan kare rayuwar dalibai ta hanyar bin ka’idojin tsaro da kare gobara.
A cikin sanarwar da hadimin shugaban kasa ya fitar, an ce:
"Shugaba Tinubu na mika ta’aziyyarsa ga gwamnatin jihar da masu makarantar, tare da yin addu’ar samun waraka ga wadanda ke jinya.”
“Shugaban kasa na kira ga dukkan makarantu masu zaman kansu da na gwamnati da su mayar da hankali kan tsaron yara a kowane lokaci, tare da umurtar hukumomin da ke kula da harkokin ilimi da su tabbatar da bin ka’idojin tsaro."
Tinubu ya yi ta’aziyyar mutuwar daliban Zamfara
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi addu’ar samun rahama ga rayukan yaran da suka riga mu gidan gaskiya sakamakon gobarar da ta tashi a tsangayar da ke jihar Zamfara.
Sanarwar da hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya fitar ta ce:
"Shugaban kasa na rokon Allah Madaukakin Sarki Ya ji kan wandanda su ka rasu, tare da bai wa iyalansu hakuri da juriyar wannan babban rashi."
’Yan sanda sun tabbatar da gobarar Zamfara
Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta tabbatar da mutuwar daliban tsangaya 17 da kuma raunata wasu 15 a gobarar da ta auku a makarantar.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Mohammed Shehu Dalijan, ya bayyana cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 2:00 n.d a ranar Laraba.
Gobarar ta tashi a makwancin daliban a lokacin da su ke bacci, inda ta tafka mummunar barna, har rayuka 17 su ka salwanta.

Kara karanta wannan
Dambarwar Albany da abubuwa 4 da suka ta da kura a kafofin sadarwa a Arewacin Najeriya
Ya ce:
"Mun samu rahoton bakin ciki cewa wasu Almajirai sun rasa rayukansu a gobarar yayin da suke barci."
Zamfara: Gwamna ya yi bakin cikin rasuwar dalibai
A baya, kun ji cewa, Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana alhinin sa kan rasuwar almajirai 17 a gobarar da ta tashi a wata makarantar Tsangaya a Kaura Namoda.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, Gwamna Lawal ya bayyana cewa lamarin abin bakin ciki ne, tare da jajantawa iyalan da suka rasa ‘yan uwansu da kuma daliban da suka jikkata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng