Cikakkun Sunaye Da Bayanan Jihohi 7 Da Ake Son Kirkira a Najeriya

Cikakkun Sunaye Da Bayanan Jihohi 7 Da Ake Son Kirkira a Najeriya

  • 'Yan majalisar dattawa da na wakilai suna ta mika bukatun kirkirar karin wasu jihohi a fadin Najeriya, musamman a shiyyar Kudu
  • An ruwaito cewa za a kirkiri jihohin ne ta hanyar zabtarar wasu kanan hukumomi daga cikin wasu jihohin da ake da su a halin yanzu
  • Sunayen jihohin suna hada da: Adada, Ife, Orlu, Anioma da sauransu, wadanda tuni kudurin dokar wasu ya tsallake karatu na biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

FCT, Abuja - Tun farkon hawan Shugaba Bola Tinubu kan mulki, majalisar dattawa take ta kokarin ganin da kawo canji a kudin tsarin mulki.

Daga cikin manyan sauye-sauyen da ake so a yi a kundin, akwai yunkurin kirkirar sababbin jihohi a yankun kudancin kasar nan.

Kara karanta wannan

"Hakurin talaka ya fara karewa": Sanatoci sun ankarar da Tinubu kan yunwa a kasa

Abin da muka sani game da jihohi 7 da aka mika bukatar kirkirarsu a Najeriya.
Cikakken bayani kan jihohi 7 da ake so a kirkira a Najeriya. Hoto: @DapoAbiodunCON
Asali: Twitter

Duk da cewa an samu sauye-sauye a kundin tsarin mulki tun dawowar dimokuradiyya a 1999, amma da alama majalisar tarayya ta 10 na son kafa nata tarihin ta hanyar kirkirar jihohin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ita ma gwamnatin tarayya ta dukufa wajen kafa tarihin da ‘yan Najeriya za su rika tunawa da ita, kamar gina titin Legas zuwa Calabar da yunkurin samar da ‘yanci ga kananan hukumomi.

Idan har za a iya cimma duk wadannan a cikin shekaru hudu na gwamnatin Tinubu, to majalisar ta 10 da shugaban kasa za su iya shiga tarihi.

Jerin jihohi 7 da ake so a kirkira

An mika bukatar kafa sabbin jihohi bakwai a gaban majalisar dattawa da majalisar wakilan Najeriya. Ga jerin jihohin:

1. Jihar Oke-Ogun

Mun ruwaito cewa jihar Oke-Ogun ta shiga jerin jihohin da ake so a kirkira daga wani sashi na jihar Oyo ta yanzu. Za ta hada da karin kananan hukumomi 12.

Kara karanta wannan

An sha dakyar: Wutar lantarki ta gyaru, an ga dawowar wuta a wasu jihohin Najeriya

Kananan hukumomin sun hada da Olorunsogo, Irepo, Oorerelope, Ogbomosho ta Arewa, Ogbomosho ta Kudu, Saki ta Gabas, Saki ta Yamma, Atisbo, Itesiwaju, Iwajowa, Kajola, da Iseyin.

2. Jihar Ijebu

Dan majalisar wakilan tarayya, Oluwole Oke daga jihar Osun ya gabatar da kudirin ƙirƙirar jihar Ijebu, wadda ake son fitar da ita daga jihar Ogun ta yanzu.

Kananan hukumomin da za ta kunsa sun hada da: Ijebu ta Gabas, Ijebu ta Arewa maso Gabas, Ijebu Ode, Ikenne, Odogbolu, Ogun Waterside, Remo ta Arewa, Sagamu, da wani sashi na Abeokuta.

3. Jihar Ife-Ijesa

Wata jihar da dan majalisar na Osun ya mika bukatar kirkira ita ce Ife-Ijesa, wacce za a cire daga jihar Osun.

Jihar za ta kwashe kanan hukumomi tara na jihar Osuna. Sun hada da: Atakunmosa ta Gabas, Atakunmosa ta Yamma, Boluwaduro, Ife ta Tsakiya, Ife ta Gabas, Ife ta Arewa, Ife ta Kudu, Ilesa ta Gabas, da Ilesa ta Yamma.

Kara karanta wannan

Shinkafi ya fadi abin da ke kawo rashin tsaro a Arewa maso Yamma, ya ba da mafita

4. Jihar Adada

Jihar Adada kuwa za ta samu ne daga yankin Enugu ta Arewa kuma Sanata Okey Ezea ya mika bukatar gaban majalisa, kamar yadda muka ruwaito.

Za ta kafu ne da kananan hukumomi shida da suka hada da: Igbo-Eze ta Arewa, Igbo-Eze ta Kudu, Udenu, Nsukka, Igga, da Uzo-Uwani.

5. Jihar Etiti

An mika bukatar kirkirar jihar Etiti ne a ranar 2 ga Yulin 2024. Za a samar da ita ne ta hanyar cireta daga jihohin Ebonyi, Enugu, Anambra, Abia da Imo.

'Yan majalisa biyar ne suka mika wannan bukatar. Su ne: Miriam Onuoha, Chinwe Nnabuife, Amobi Ogah, Anayo Onwuegbu, da Kama Nkemkama.

6. Sauran jihohin biyu

Sauran jihohin biyu da aka mika bukatar kirkirarsu sun hada da Orlu da Anioma.

Jihar Orlu za ta mallaki kananan hukumomi ashirin da takwas, yayin da jihar Anioma za ta mallaki kananan hukumomi tara.

Kara karanta wannan

Jihar Adada: Muhimman abubuwa 5 game da shirin kirkirar sabuwar jiha a Kudu maso Gabas

Tinubu ya kirkiri sabuwar ma'aikata

A wani labari na daban, mun bayyana cewa, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kirkiri sabuwar ma'aikata a Najeriya.

An bayyana sunan ma'aikatar da 'ma'aikatar bunkasa kiwon dabbobi'. Hakan baya rasa alaka da son magance rikicin manoma da makiyaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.