Alau: Gwamnatin Tinubu Ta Amince da Aikin N80bn a Borno, Ta Fadi Lokacin Farawa
- Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta waiwayi aikin gyara madatsar ruwa ta Alau a jihar Borno
- A yayin zaman majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) da Bola Tinubu ya shugabanta, an amince da N80bn domin gudanar da aikin
- Ministan albarkatun ruwa da tsaftar muhalli, Joseph Utsev, ya bayyana cewa za a kammala aikin a cikin watanni 24
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta amince da Naira biliyan 80 don sake ginawa da gyara madatsar ruwa ta Alau a jihar Borno.
A shekarar da ta gabata ne dai madatsar ruwan ta Alau ta ɓalle, wanda hakan ya jawo mummunar ambaliyar ruwa a birnin Maiduguri da wasu garuruwan.

Asali: Facebook
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin shugaba Bola Tinubu, Dada Olusegun, ya sanya a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Tinubu za ta gyara madatsar ruwan Alau
Ministan albarkatun ruwa da tsaftar muhalli, Joseph Utsev ya bayyana amincewar a ƙarshen taron FEC da Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a ranar Talata a fadar shugaban ƙasa.
Joseph Utsev ya ce gwamnatin jihar Borno ta yi haɗin gwiwa da gwamnatin tarayya don fara aikin, wanda za a kammala cikin watanni 24 masu zuwa.
Ya ƙara da cewa, aikin gyaran farko na madatsar ruwan zai gudana a tsakanin watan Fabrairu da Yuli domin tabbatar da cewa ba a samu ambaliyar ruwa a jihar ba a wannan shekarar.
“Na bayar da rahoto kan kwamitin da aka kafa a ranar 23 ga Satumba 2024 kan tantance madatsun ruwa a Najeriya. An ƙaddamar da kwamitin a ranar 2 ga watan Oktoba 2024."
“Shugaban ƙasa ya amince da Naira biliyan 80 don sake ginawa da gyara madatsar ruwa ta Alau a jihar Borno, kuma wannan yana jiran amincewar FEC yayin da ake bin dukkanin hanyoyin da suka dace."
"Ana aiki tare da gwamnatin jihar Borno don fara aikin tsakanin yanzu da watan Yuli 2025. Za a fara da sashi na farko don tabbatar da cewa ambaliya ba ta faru ba a jihar Borno a cikin 2025, aikin zai kammala cikin watanni 24 masu zuwa."
- Joseph Utsev
Gwamnati ta ɗauki mataki bayan ambaliya
A ranar 9 ga watan Satumba 2024, fiye da mutane 30 ne suka mutu sannan mutum 400,000 suka rasa matsuguni sakamakon ambaliya a Maiduguri, jihar Borno, saboda ɓallewar madatsar ruwa ta Alau, cewar rahoton TheCable.
Bayan ɓallewar madatsar ruwan, gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin tantance lafiyar dukkanin madatsun ruwa a ƙasar, ciki har da Alau.
Kwamitin, wanda Joseph Utsev ke jagoranta, ya bayyana cewa sun ɗauki madatsar ruwan Alau a matsayin ta farko mafi muhimmanci da ya kamata a sake ginawa bisa ga tantancewar da suka yi.
Tinubu ya ƙi amincewa da kafa jami'a
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙi rattaɓa hannu kan dokar da za ta kafa jami'ar ilmi ta tarayya a jihar Adamawa.
Shugaban ƙasan ya bayyana cewa akwai kura-kurai a cikin dokar, wanda hakan ne ya sanya ya ƙi amincewa da ita.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng