Shugaba Tinubu Ya Ki Amincewa da Kafa Sabuwar Jami'a a Arewa, Ya Fadi Dalili
- Batun kafa sabuwar ilmi ta tarayya a jihar Adamawa ya gamu da cikas a wajen Mai girma shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
- Shugaban ƙasar ya ƙi amincewa da dokar kafa sabuwar jami'ar ilmi ta tarayya a garin Numan da ke jihar Adamawa a Najeriya
- Mai girma Bola Tinubu ya bayyana dalilinsa na ƙin amincewa da dokar a cikin wata wasiƙa da ya aika zuwa ga majalisar wakilai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙi amincewa da kudirin da za ta kafa jami'a a jihar Adamawa.
Shugaba Bola Tinubu ya ƙi amincewa ne da dokar za ta kafa jami'ar ilmi ta tarayya da ke Numan, a jihar Adamawa.

Asali: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce ya sanar da hakan ne a cikin wata wasiƙa da ya aikawa shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajuddeen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu, ne ya karanta wasiƙar a yayin zaman majalisar na ranar Talata, 4 ga watan Fabrairun 2025, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
Meyasa Tinubu ya ƙi amincewa da dokar?
A cikin wasiƙar, Shugaba Tinubu, ya yi bayani kan dalilinsa na ƙin amincewa da dokar da za ta kafa jami'ar.
Ya ce daga cikin dalilan akwai cewa sashe na 22 na dokar ya ba da iko kan filin ga gwamnan jihar, maimakon shugaban ƙasa kamar yadda doka ta tanada dangane da batun filayen jami'o'in gwamnatin tarayya.
Benjamin Kalu ya ƙara da cewa, Shugaba Tinubu ya kuma bayyana a cikin wasikar cewa, an cire batun ba da digiri a cikin sashe na 25(b) na dokar wacce ake son kafa jami'ar.
Majalisa ta miƙa kudirin gaban Tinubu
Majalisar wakilai ta gabatar da dokar a shekarar da ta gabata, ta amince da kafa jami'ar ilmi ta tarayya a Numan a jihar Adamawa, sannan ta miƙawa shugaban ƙasa domin amincewa.
Shugaban ƙasa Tinubu, bisa tanadin da ke cikin kundin tsarin mulkin ƙasa, yana da hakkin ƙin amincewa da kowace doka da majalisa ta gabatar.
Wannan lamarin ya kasance mai muhimmanci domin yana nuna matsayin shugaba Tinubu kan batutuwan da suka shafi kafa sababbin jami'o'i a ƙasar, da kuma yadda zai tabbatar da cewa dokokin da aka gabatar suna da cikakken daidaito da tsarin mulkin ƙasa.
Wannan ƙin amincewar da shugaba Tinubu ya yi, zai ba da damar ƙara tattaunawa a majalisa da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki, domin ganin yadda za a magance waɗannan batutuwa kafin a sake gabatar da dokar.
Tinubu ya amince a kafa jami'a
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince a kafa sabuwar jami'a a jihar Rivers da ke yankin Kudu maso Ƙudu na Najeriya.
Shugaba Tinubu ya amince a kafa sabuwar jami'ar ne ta fasahar muhalli a Ogoni da ke cikin jihar Rivers.
Amincewa da kafa jami'ar na cikin ƙoƙarin da gwamnatin Tinubu ke yi na ganin an samu wadataccen ilmi a kowane yanki na Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng