Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa da Ministoci da Manyan Ƙusoshin Gwamnati a Abuja
- Shugaba Bola Tinubu yana jagorantar zaman FEC a Abuja don duba muhimman takardu bayan zaman farko na majalisar a 2025
- Majalisar ta amince da Naira biliyan 4.8 don samar da fakitin maganin cutar kanjamau guda 150,000 daga Fabrairu zuwa Mayu 2025
- Mataimakin shugaba, Sanata Kashim Shettima, shugaban ma'aikatan Aso Villa, Femi Gbajabiamila da ministoci sun halarci taron
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana jagorantar zaman majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) a fadar gwamnati da ke Abuja.
Wannan zama na yanzu ya biyo bayan taron majalisar na farko a shekarar 2025 wanda aka fara gudanar da shi a jiya Litinin.

Asali: Facebook
Tinubu ya jagoranci taron majalisar FEC
Rahoton The Nation ya nuna cewa an fara zaman majalisar FEC din ne da ƙarfe 1:26 na rana bayan isowar Bola Tinubu cikin ɗakin taron majalisar.

Kara karanta wannan
Bayan shawarar gwamnoni, majalisa za ta zauna domin tabbatar da kudirin haraji da gaggawa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan watsa labarai da wayar da kan al’umma, Mohammed Idris, ya sanar da manema labarai cewa taron majalisar zai kasance na kwana biyu.
A jiya Litinin, Mohammed Idris ya ce:
“Zaman majalisar zai ci gaba gobe saboda akwai muhimman takardu masu yawa da suka taru tun watan Disamba da ake son duba su."
Kusoshin gwamnati da suka halarci taron
Ministan ya ci gaba da cewa:
“Shugaban ƙasa ya na son a kammala duba dukkanin takardun don ci gaba da aiwatar da ayyukan gwamnati yadda ya kamata."
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, da shugabar ma’aikatan gwamnati, Didi Walson-Jack sun halarci taron.
Haka zalika, mahalarta taron sun hada da shugaban mma’aikatan fadar gwamnati, Femi Gbajabiamila da ministoci daban-daban na tarayya.
Gwamnati za ta kashe N4.5bn kan maganin HIV
A wani labarin, mun ruwaito cewa, majalisar zartarwa ta tarayya ta amince a kashe N4.5bn domin sayen magungunan cutar HIV har fatiki 150,000.

Kara karanta wannan
'Za mu iya': Tinubu ya dauki mataki da Amurka ta janye tallafin yaki da cutar HIV
Ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Ali Pate, ya bayyana cewa kudurin ya biyo bayan tattaunawa kan tasirin sauye-sauyen manufofin Amurka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng