Jami'an Tsaro Sun Nuna Kwarewa, Sun Ceto Mutanen da 'Yan Bindiga Suka Sace a Kaduna
- Ƴan bindigan da suka yi garkuwa da wasu mutane a ƙaramar hukumar Kajuru sun ji a jikinsu a hannun jami'an tsaro
- Jami'an tsaron da suka haɗa da sojoji da ƴan sanda sun ragargaji ƴan bindigan tare da samun nasarar kuɓutar da mutum 23 da suka sace
- Kwamishinan ƴan sandan jihar Kaduna ya ba da tabbacin cewa za su ci gaba da aiki tuƙuru domin kare rayuka da dukiyoyin al'umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Jami’an tsaro na ƴan sanda da sojoji sun samu nasarar ceto mutane 23 da aka yi garkuwa da su a jihar Kaduna.
Jami'an tsaron sun ceto mutanen ne waɗanda aka sace, a lokacin wani samame na haɗin gwiwa da suka kai a yankin ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar.

Asali: Twitter
Tashar Channels tv ta ce mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya tabbatar da ceton mutanen a ranar Lahadi a cikin wata sanarwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami'an tsaro sun ragargaji ƴan bindiga
A cikin sanarwar, ya bayyana cewa DPO na ƴan sandan Kajuru tare da dakarun sojoji sun kai farmaki kan gungun ƴan bindiga bayan samun sahihan bayanai cewa suna ƙoƙarin kwashe mutanen da suka sace zuwa dajin Kajuru.
A yayin artabun, jami’an tsaro sun yi wa ƴan bindigan ruwan wuta, wanda ya tilasta musu tserewa cikin daji ɗauke raunukan harbin bindiga, lamarin da ya ba da damar kuɓutar da mutum 23 da suka yi garkuwa da su.
A cewar rundunar ƴan sandan, an mayar da mutanen da aka ceto cikin ƙoshin lafiya zuwa ga iyalansu, yayin da aka ƙara tsaurara matakan tsaro a yankin, tare da gudanar da sintiri don hana sake aukuwar irin hakan.
Ƴan sanda sun ba da tabbaci
Hazalika, kwamishinan ƴan sandan jihar Kaduna, CP Rabiu Muhammad, ya tabbatar da cewa rundunar tana nan daram wajen tabbatar da tsaron lafiyar al’ummar jihar, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
Ya kuma jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da aiki tare da gwamnatin jihar, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Uba Sani, don ganin an magance matsalolin tsaro a jihar gaba ɗaya.
Ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da bayar da hadin kai ga jami’an tsaro ta hanyar bayar da ingantattun bayanai da za su taimaka wajen murƙushe ayyukan ƴan ta’adda a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.
Ƴan sanda sun cafke masu ba ƴan ta'adda babura
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an ƴan sanda sun samu nasarar cafke wasu mutane da ake zargi da samarwa ƴan ta'addan Boko Haram, babura a jihohin Neja da Kaduna.
Mutanen dai sun shigo hannu ne bayan an samu bayanan sirri kan yadda suke satowa tare da siyar da babura ga ƴan ta'addan masu tayar da ƙayar baya.
Bayan cafke su, ƴan sandan sun samu nasarar ƙwato babura masu yawa a hannunsu waɗanda suka yi niyyar kai wa ƴan ta'addan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng