Gwamnatin Tinubu za Ta Kashe Naira Biliyan 885 domin Ayyukan Tituna 10

Gwamnatin Tinubu za Ta Kashe Naira Biliyan 885 domin Ayyukan Tituna 10

  • Majalisar zartarwa ta kasa ta amince da kashe Naira biliyan 885 domin inganta hanyoyin mota da gadoji a sassan Najeriya
  • An amince da Naira biliyan 252 domin aikin hanyar Abuja-Kano, tare da sake gina sassa uku na hanyar Lokoja-Benin
  • Majalisar ta amince da ware Naira biliyan 470.9 don yankin Delta da Naira biliyan 148 domin aiki a bangaren Anambra

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Majalisar zartarwa ta kasa (FEC) karkashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta amince da kashe Naira biliyan 885 domin aiwatar da ayyukan tituna guda 10.

Da yake jawabi bayan taron FEC da aka gudanar a ranar Litinin a Abuja, Ministan ayyuka, David Umahi, ya bayyana cewa wadannan ayyuka na da nufin inganta hanyoyin mota da gadoji a jihohi daban-daban na Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba Gida Gida ta fadi dalilin kashe N2.5bn a kan auren gata

Tinubu
Gwamnati za ta kashe biliyoyin Naira wajen gyaran hanyoyi Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

The Cable ta ruwaito cewa ya jaddada wasu manyan ayyuka da aka amince da su, ciki har da sake gina sassa uku na hanyar Lokoja-Benin, wata muhimmiyar hanya ga kasuwanci da sufuri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kano za ta samu titin gwamnatin tarayya

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa Umahi ya bayyana cewa an amince da Naira biliyan 252 domin aikin gyaran hanyar Abuja zuwa Kano, wanda aka tsara a raba shi zuwa manyan sassa guda biyu.

Ministan ya ce:

"Za a yi aikin ne da siminti kuma za a yi: daga Obajana zuwa Benin (Sashi na I) za a kashe Naira biliyan 64, daga Auchi zuwa Edo (Sashi na II) Naira biliyan 110, sannan daga Filin Jirgin Sama na Benin zuwa Edo (Sashi na III) Naira biliyan 131. Jimillar kudin aikin ya haura Naira biliyan 305."

A cewarsa, sashi na farko zai fara daga iyakar FCT zuwa Niger, tare da karin hanyar mai tsawon 5.71 km, yayin da sashi na biyu zai ratsa wasu yankuna a jihar Kano da karin tsawon 17 km.

Kara karanta wannan

'Da yanzu abinci ya gagari talaka': Yadda CBN ya ceto tattalin Najeriya a 2024

Ya kara da cewa mafi yawan aikin za a yi shi ne da siminti, tare da sanya fitilun hasken rana a kan hanyar mai tsawon 118 km.

Gwamnati za ta gina gadar kogi

Majalisar ta kuma amince da sake gina hanyoyin shiga gadar Niger ta biyu da ke tsakanin jihohin Delta da Anambra.

Ministan ya ce:

"Za a gina bangaren jihar Delta da siminti, kuma kudin aikin zai kai Naira biliyan 470.9, yayin da bangaren jihar Anambra zai ci Naira biliyan 148."

Gwamnati za ta kashe N3bn don duba gadoji

Umahi ya bayyana cewa an amince da Naira biliyan 3.571 domin gudanar da cikakken bincike kan tsaron gadojin Third Mainland da Carter Bridges a Legas.

Ministan ya ce tantancewar zai mayar da hankali ne kan duba karfin gadojin da ke karkashin ruwa da gano hanyoyin da za a bi don hana su tabarbarewa.

Gwamnati ta musanta kara kudin wuta

A baya, mun ruwaito cewa gwamnatin Tarayya ta yi karin haske kan batun karin farashin wutar lantarki, bayan da aka samu rahotannin da ke nuna cewa za a yi karin 65% na kudin wuta.

Kara karanta wannan

Jikin tsohon gwamnan Taraba ya rikice, kotu ta ba shi damar neman lafiya, an tono barnarsa

Olu Arowolo Verheijen, mai ba da shawara kan makamashi ga shugaba Bola Tinubu, ta bayyana cewa an yi kuskuren fahimtar kalamanta a wata hira da ta gabata, inda ta ce babu batun karin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.