Tinubu Ya Kyale 'Yan Adawar Arewa, Ya Rattaba Hannu kan Dokar Kafa Hukumar NCDC
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan sabuwar dokar kafa hukumar raya yankin Arewa ta Tsakiya (NCDC)
- Ana sa ran dokar kafa NCDC za ta taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki da samar da ayyukan ci gaba a yankin Arewa ta Tsakiya
- Baya ga dokar kafa NCDC, Tinubu ya kuma amince da kafa kwalejin kimiyya a Rano (Kano), da jami’ar lafiya a Tsafe (Zamfara)
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan kudirin dokar kafa hukumar raya shiyyar Arewa ta Tsakiya (NCDC).
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana rattaba hannun dokar a zaman majalisar dattawa na ranar Talata.

Asali: Twitter
Tinubu ya rattaba hannu kan kafa hukumar NCDC
Dama ba tun yanzu ake ta kiraye-kiraye ga shugaban ƙasa ya rattaba hannu kan kudirin kafa hukumar raya yankin Arewa ta Tsakiya ba inji rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An rahoto cewa dokar za ta ƙarfafa tattalin arziki da bunƙasa samuwar ayyukan ci gaba a yankin Arewa ta Tsakiya.
Har ila yau, shugaban majalisar dattawan ya ce Tinubu ya rattaba hannu kan dokar kafa kwalejin kimiyya da fasaha a Rano da ke Kano da jami’ar kiwon lafiya a Tsafe da ke Zamfara.
Akpabio ya aika sako ga 'yan Arewa ta Tsakiya
Akpabio ya ce:
“Ina sanar da ku cewa shugaban ƙasa ya amince da dokar kafa Hukumar Raya shiyyar Arewa ta Tsakiya don kawo ci gaba ga yankin.”
Jaridar The Nation ta rahoto shugaban majalisar ya kuma taya mutanen yankin Arewa ta Tsakiya murna, yana fatan za su mori wannan ci gaban.
Akpabio bai bayyana ranar da Tinubu ya rattaba hannu kan dokar ba, amma sanarwar ta biyo bayan amincewar Tinubu da kafa jami’ar fasahar muhalli a Ogoni, jihar Ribas.
Tinubu ya nada shugabannin hukumar NWDC
A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaba Bola Tinubu ya naɗa 'yan majalisar gudanarwa na Hukumar raya Arewa maso Yamma (NWDC).
Shugaban ƙasar ya aika sunayen mutum tara da ya naɗa a hukumar ga majalisar dattawa domin tantancewa da tabbatar da naɗinsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng